Fulham ta kammala ɗaukar Cuenca daga Villareal

Jorge Cuenca

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Fulham ta kammala sayen ɗan wasan tawagar Sifaniya, Jorge Cuenca daga Villarreal kan kudin da ba a bayyana ba.

Ɗan wasan mai shekaru 24, ya amince da kwantiragin kaka hudu a Craven Cottage tare da cewar za a iya tsawaita masa kaka ɗaya, idan ya taka rawar gani.

Cuenca, wanda ya buga wa Sifaniya tamaula tun daga matasa har zuwa matakin ‘yan kasa da shekara 21, ya fara taka leda a Alcorcon da Barcelona daga nan ya koma Villarreal.

Ya buga wasa 37 a kakar da ta wuce, inda Villareal ta kare a matsayi na takwas a gasar La Liga da kai wa matakin ƴan16 a gasar cin kofin Europa.

Haka kuma Fulham ta kammala sayan ɗan wasan Arsenal, Emile Smith Rowe a ranar Juma'a kan fam miliyan 27.

Ryan Sessegnon shi ma ya koma Fulham a bana kan kwantiragin kaka biyu, bayan da yarjejeniyarsa ya kare a Tottenham.

Haka kuma Fulham na son sayen ɗan wasan Manchester United, Scott McTominay, kan kuɗin da ake cewa zai kai fam miliyan 20 ga ɗan Scotland mai shekaru 27.