Abin da ya sa ake kai ruwa rana tsakanin matasa da masu mulki a soshiyal midiya

..
An wallafa

Ɗaya daga cikin abubuwa masu muhummanci da ƙarni na 21 ya kawo duniya shi ne intanet.

Intanet dai ya bayar da dama ga mutane daga ko ina a fadin duniya su riƙa aika saƙonni da tattaunawa da kasuwanci da sauran abubuwan amfani na rayuwa.

Sai da a duniyar ta intanet, wani abu da jama'a suka fi amfani da shi shi ne soshiyal midiya, inda a nan ne talaka da mai kuɗi, manya da yara kan hadu domin tattaunwa da aika sakonni.

Sakamakon tasirin kafafen sada zumunta na zamani, ta kai ta kawo duk wani abu na yau da kullum da ake gudanarwa ana yin sa a can, tun daga karatu zuwa kasuwanci da siyasa har ma da aikata laifuka.

Ganin cewa ana amfani da soshiyal midiya wurin siyasa, ya sa 'yan takara da masu mulki kan shiga domin bayyana manufofinsu, mabiya kuma su bayyana bukatansu da kokensu inda a nan ne akasari akan ga koken mabiyan domin biya musu bukatunsu.

Sai dai a halin yanzu akan samu takun-saƙa tsakanin masu mulki da mabiya musamman matasa inda sukan soki masu mulki ta hanyar rubutu ko shaguɓe ko kuma su yi bidiyo su yi musu tas.

Wasu shugabannin sukan haƙura kuma su shanye duk wani cin mutunci da aka yi musu inda wasu kuma kan nuna fushin su a fili.

Misali, Patience Jonathan, uwar gidan tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ta sha suka a kafafen watsa labarai ba dare ba rana.

An rinƙa sukar duk wani motsi da ta yi a zamanin mulkin mai gidanta a kafofin sada zumunta amma ba safai ake jin ta fito ta mayar da martani ba.

Sai dai wasu shugabannin da iyalansu da suke ganin an kai su bango sukan fusata su mayar da martani. Hakan ne ya faru ga wani matashi da ake zargi mai dakin shugaban Najeriya Aisha Buhari ta sa an kama shi saboda ya yi batanci a gare ta.

Mun yi waiwaye kan wasu lokuta da aka kai ruwa rana tsakanin matasa masu amfani da soshiyal midiya da kuma shugabanni:

Sanata Musa da wani matashi Shafi'u

Caccar-bakin da ta faru tsakanin tsohon Sanata na Jihar Neja Sanata Ibrahim Musa da kuma wani matashi wanda ake kira Shafi'u ta tayar da hankali matuƙa.

Kamar yadda wani saƙon murya ya nuna, sanatan ya kira matashin inda yake zarginsa da yin rubutu a soshiyal midiya ya zage shi.

Daga nan ne aka soma cacar-baka tsakaninsu har ta kai ga zage-zage da yi wa juna barazana.

Unique Pikin da Gwamna Ganduje

.

Asalin hoton, Unique Pikin

A kwanakin baya ne wata kotu ta samu wasu masu barkwanci a shafin TikTok da laifin ɓata suna ga Gwamna Ganduje na Kano.

Gwamnan ya kai su kotu ne bayan shi Unique Pikin ɗin wanda aka fi sani da Mubarak Isa Muhammad da abokinsa  Nazifi Muhammad Bala suka shirya wani gajeren bidiyo na barkwanci inda suka zargi gwamnan da cewa ba ya barin filaye a Kano da kuma yawan bacci.

Hakan ya ja kotu ta yanke musu hukuncin bulala da kuma saka su sharar kotu na wani lokaci.

Sanata Bulkachuwa da wani matashi

.

Asalin hoton, Sanata Bulkachuwa

A kwanakin baya an yi cacar baki tsakanin Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa wanda shi ke wakiltar arewacin Bauchi da wani matashi da ke mazaɓar shi.

A wani saƙon murya da ya rinƙa yawo a shafukan sada munta an ji sanatan ya fusata bayan matashin ya harzuƙa shi.

Tun farko matashin ya nemi sanatan ya samo masa aiki amma daga baya cacar baki tsakaninsu ta kaure inda sanatan ya nuna ba aikinsa bane samar masa aiki.

Me masana ke cewa kan wannan lamari?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Takun saƙa ta baya-bayan nan da aka samu tsakanin masu mulki a soshiyal midiya da kuma mabiya shi ne kan kalaman da ake zargi wani matashi ya yi ga uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, lamarin da ya ja aka kama matashi.

Bisa wannan BBC ta tuntuɓi Maude Rabiu Gwadabe wanda masani ne kan harkar sadarwa a fagen siyasa kuma ya bayyana cewa akasari dalilin da ya sa ake samun hakan borin kunya ne.

"Ƴan siyasa su kan yi mu'amala da mabiyansu ba tare da wata yarjejeniya ba sai abin da suke kira igiyar zato, wato mutum yana bin ɗan siyasa yana fatan idan an yi nasara zai samu wani abu.

"Shi ya sa suke bin su da manufar idan ɗan siyasa ya canza riga su canza hula, idan ya canza gida su yi wa nasu fenti," in ji Maude Rabiu.

Ya bayyana cewa idan duka waɗannan abubuwan ba su samu ba ga ƴan soshiyal midiya sai su dawo kafafen sada zumuntar cikin jama'a su nemi su kunyata wannan ɗan siyasa.

Ya bayyana cewa idan wani ɗan soshiyal midiya ya caccaki ɗan siyasa sai shi kuma ya soma tunanin wane ne wannan yaron, mene ne matsayinsa ina ya kai? Idan bai kai zuciya nesa ba sai ya nemi mayar da martani kan mabiyin.

A cewarsa, ƴan siyasa sun fi mayar da martani idan an zage su a soshiyal midiya fiye da rediyo domin kuwa wani lokacin iyalansu ne kan nuna ɓacin ransu wanda hakan kan harzuƙa ɗan siyasa.

Ya bayyana cewa a hakan ne wasu lokutan ɗan siyasan ya kan nemi ya mayar da martani domin ya burge iyalansa