Iyayen matashin da jami’an tsaro suka ‘kama’ sun bai wa Aisha Buhari hakuri

Asalin hoton, OTHER
Iyayen dalibin Jami’ar nan da ake zargin jami’an tsaro daga fadar shugaban Najeriya sun kama tare da tsare shi cikin sirri tsawon kwanaki ba tare da shari’a ba, sun bukaci uwargidan shugaban kasar, Aisha Buhari,da ta yi hakuri ta yafe wa dan nasu.
Iyayen Aminu Adamu Mohammed sun ce an kama ɗan nasu ne bisa zargin wasu kalamai da ya yi ga uwargidan shugaban ƙasar na Najeriya a cikin watan Yuni.
Wata majiya a Jami'ar Tarayya ta Dutse da ke jihar Jigawa, inda aka yi awon-gaba da ɗalibin, ta ce jami'an tsaron sun yi kamen ne ba tare da sanin hukumomin makaranta ba.
Mahaifan ɗalibin, da ke aji huɗu a Jami'ar Tarayya ta Dutsen sun ce kama Aminu Adamu Mohammed ya jefa su cikin tashin hankali da kwanan zulumi.
Sun ce sai da aka shafe tsawon kwanaki kafin su samu labarin ɓacewarsa.
Daga bisani ne, aka kira mahaifin ɗalibin don shaida masa cewa Aminu yana tsare a Abuja.
Iyayen Aminu sun ce an kama ɗansu ne tun ranar Alhamis 17 ga wata, inda aka ci gaba tsare shi tsawon kwanaki, bayan an lakaɗa masa duka a fadar shugaban ƙasa.
Shehu Baba Azare, shi ne ƙanin mahaifin Aminu Adamu, ya shaida wa BBC cewa, su fatansu shi ne ayi hakuri a sakar musu dansu.
Ya ce,” Uwargidan shugaban kasa kiyi hakuri ki saki tun da ke uwace, wannan shi ne abin da muke fata.”
Wata majiya a Dutse ta ce kama Aminu Adamu ya yi matuƙar ta da hankali a jami'ar da ma a tsakanin iyayen ɗalibai, la'akari da halin taɓarɓarewar tsaro da ake ciki.
Rahotanni sun ce kama matashin ba ya rasa nasaba da wani rubutu da ya yi cikin watan Yuni a shafinsa na tuwita, inda aka yi zargin ya sa hoton matar shugaban ƙasa, inda ya zarge ta da cin kuɗin talakawa, kuma ya tanka ta.
Mutane da yawa sun soki lamirin Aminu da cewa abin da ya yi bai dace ba, don kuwa ba lallai ne yana da hujjar zargin da ya yi wa Aisha Buhari ba. Yayin da wasu ke cewa kama shi da tsare shi a sirrance ba tare da an kai shi kotu ba, shi ma keta doka ne.
Kuma bai kamata a samu hakan daga iyalin shugaban ƙasa ba.
Tuni ƙungiyoyin kare 'yancin ɗan'adam kamar Amnesty International suka sa baki a gangamin neman a saki Aminu Adamu.
Matashin a cewar Shehu Baba Azare, na gab da fara rubuta jarrabawarsa ta ƙarshe a jami'a, kafin faruwar lamarin.











