Wolves ta yi watsi da tayin Man City kan Matheus Nunes.

Matheus Nunes

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Wolves ta ki amincewa da tayin fan miliyan 47 da Manchester City ta yi wa dan wasan tsakiyar Portugal Matheus Nunes.

Wolves ta dauko dan wasan mai shekaru 24 a kan kwantiragin shekara biyar a bazarar da ta wuce, inda ta biya Sporting Lisbon fam miliyan 38.

City ta so ta karfafa bangaren 'yan wasan tsakiyarta tun kafin Kevin De Bruyne ya samu rauni a kafarsa wanda zai iya sa ya yi jinyar watanni huɗu.

Kungiyar da guardiola ke jagoranta na sha'awar ɗaukar ɗan wasan Crystal Palace Eberechi Eze, mai shekara 25, wanda ya fara buga wa Ingila wasa a watan Yuni.

City ta kuma yi zawarcin dan wasan West Ham Lucas Paqueta kafin a bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta Ingila na binciken dan kasar Brazil din mai shekara 25 kan laifin keta ka'idojin yin caca.

Wolves ba ta son rasa Nunes kar ta shiga tsaka mai wuya wurin nemo mai maye gurbinsa yayin da ya rage mako guda a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa.