Matasan Najeriya na cikin halin gaba-kura-baya-sayaki kan ficewa daga ƙasar

Olotu Olanrewaju
Bayanan hoto, Olotu Olanrewaju, na daga cikin dubban matasan Najeriya da ke tunanin ficewa daga ƙasar zuwa ƙetare domin neman arziƙi
    • Marubuci, Hannah Gelbart
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC What in the World, Lagos
  • An wallafa

Olotu Olanrewaju wani matashi ne, da ya kammala karatun digirinsa a Najeriya, ya gaza yanke shawara kan ko ya zauna a ƙasarsa da yake matuƙar ƙauna ko kuma ya tsallake zuwa wata ƙasar domin neman kyakkyawar rayuwa.

Yana alfahari da al'adunsa, da abinci da kuma iyalansa, musamman yadda ƴan'uwa kan riƙa kula da nuna damuwa da juna.

To amma matashin mai shekara 24 a duniya, wanda ya yi karatun ilimin sarrafa lantarki na ganin cewa ba ya samun damar da ta dace wajen amfani da iliminsa.

"Ina neman inda zan samu rayuwa mai kyau da kuma damarmaki, a maimakon na cushe kaina wuri ɗaya a nan Najeriya," kamar yadda ya shaida wa BBC a cikin wani shirin Podcast.

Ya ƙara da cewa yana da tabbacin cewa digirinsa "zai fi amfani " a ƙasashen waje.

Akwai kuma damuwar cewa rashin abubuwan more rayuwa - lamarin da ke haifar da katsewar lantarki - da kuma rashin tsaro da rashawa da rashin kyakkyawan shugabanci duk suna zama ƙalubale ga ci gaban rayuwar al'umma.

Mista Olanrewaju na cikin dubun dubatar matasa, da sauran al'ummar Najeriya waɗanda suka fitar da rai da ƙasar, waɗanda ke tunanin ficewa daga ƙasar zuwa ƙasashen ƙetare.

Wannan wani abu ne da ya samu karɓuwa kuma ake yayinsa a ƙasar, inda ake masa laƙabi da "japa", daga wata kalmar Yarbanci wadda ke nufin "tserewa".

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

BBC ta tuntuɓi jami'an gwamnati da dama domin jin martaninsu kan abin da matasan suka shaida mana, sai dai jami'an gwamnatin ba su ce mana komai ba.

Sai dai batun al'ummar Najeriya da ke tserewa daga ƙasar ba sabon abu bane.

Tun daga shekarun 1980, da dama daga cikin al'ummar ƙasar masu matsakaicin ƙarfi sun riƙa neman tsallakawa ƙasashen ƙetare domin neman arziƙi.

To amma a halin yanzu lamarin ya yi ƙamari tsakanin matasa da ake yi wa laƙabio da 'Gen Z'.

Wani bincike da cibiyar African Polling Institute ta gudanar daga shekarar 2022 ya gano cewa kashi 69 cikin ɗari na ƴan Najeriya waɗanda shekarunsu suka kama daga 18 zuwa 35 na son ficewa daga ƙasar da zaran suka samu damar hakan - duk kuwa da ɗan raguwa da aka samu na alƙaluman a 2021. A 2019 alƙaluman sun nuna cewa kashi 39 cikin ɗari ne kawai.

A shafukan sada zumunta za ka ga yadda matasa ke wallafa bayanai game da halin da suke cikin bayan ficewa daga ƙasar.

Yayin da wasu ke cewa suna kewar gida, wasu kuma na nuna alfanun da suka samu bayan ficewa daga ƙasar, tare da ƙarfafa wa ƴan'uwansu matasa su ma su yi hakan.

Sai dai ficewa daga ƙasar abu ne mai tsada.

Tsadar rayuwa da ke ƙara muni, da zubewar darajar takardar naira ya sa lamarin ya yi tsada sosai kuma ya zama mai wahala - sai dai hakan na ci gaba da ingiza mutane a ƙoƙarinsu na ganin sun fice daga ƙasar.

Koyon Jamusanci

Ficewa zuwa ƙasashen ƙetare ya fi sauƙi ga mutanen da suka kammala digiri waɗanda suka ƙware a wani fanni, inda sukan samu ayyukan yi masu kyau a ƙasashen Yamma, ta yadda za su samu kuɗin da za su iya rayuwa a ƙasashe waɗanda tsadar zama a can ta fi ta gida Najeriya.

Baya ga masu bin ƙa'ida wajen ficewa daga ƙasar, akwai kuma waɗanda ke ƙoƙarin amfani da ɓarauniyar hanya ta hanayr tsallaka hamadar sahara ko kuma tekun meditaraniya.

Dubban irin wadannan matasa ne ke mutuwa a irin wannan hanya, kuma kadan daga cikinsu da kan samu nasrar tsallakawa kan yi ta fadi tashi ba tare da sun samu aikin yi ko kuma muhalli mai kyawu ba.

A nasa ɓangaren, Mista Olanrewaju da iyalansa sun kwashe shekaru suna tara kuɗi. Yana sa ran tafiya ƙasar Jamus ko Sifaniya, kuma tuni ya shiga makarantar koyon Jamusanci domin haɓɓaka damarsa ta zuwa ƙasashen.

Ba shi ne na farko a cikin iyalansa da ya bi irin wannan hanya ba.

Shekaru biyu da suka gabata, ɗan'uwansa mai suna Daniel, mai shekara 27 ya samu nasarar tsallakewa zuwa ƙasar Scotland, inda yake rayuwa a birnin Aberdeen.

Yanzu yana aiki a can a matsayin mai ɗaukan hoto da kuma kula da al'umma, kuma duk da cewa ya san abin da ɗan tsada, amma ya faɗa wa ɗan'uwansa irin alfanun da ke tattare da lamarin - kamar abubuwan more rayuwa da ake da su a Scotland, kamar isasshen lantarki da ruwa mai tsafta da kuma tsarin sufuri mai kyau.

Oluwatobi

Asalin hoton, Oluwatobi Abodunrin

Wata mai aikin kula da al'umma, Oluwatobi Abodunrin, mai shekara 29 ta koma da rayuwa a birnin Landan cikin shekarar da ta gabata, kuma tana yaba wa matakin nata.

Ta ce Najeriya na cike da "zaƙaƙuran matasa" waɗanda ke son cin gajiyar ƙwarewarsu.

Ta ce "na yanke shawarar barin Najeriya ne kasancewar ba na samun abin da nake so".

"Muna da ƙwaƙwalwa sosai, muna son a san da mu, muna son a ji muryarmu kuma muna son a martaba mu."

Amma ta amince da cewa ba abu ne mai sauƙi ba ka baro iyalanka ka taho kai kadai.

"Mataki ne mai wahala da na yanke na barin gida. Ka baro mutanen da ke saon ka, waɗanda ke tausaya maka. Amma duk da haka ina farin ciki da matakin da na ɗauka, komai na tafiya daidai."

Alƙaluman gwamnati sunnuna cewa akwai ƴan Najeriya sama da 270,000 kamar Abodunrin waɗanda ke rayuwa a Birtaniya.

Birtaniya na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da ƴan Najeriya suka fi son zuwa, inda yawan ƴan Najeriya da ke samun takardar zama da aiki a Birtaniya ya nunnunka tun daga shekarar 2019 bayan ƙasar ta fice daga Tarayyar Turai.

Sai dai Birtaniyar ta ɗauki matakin daƙile wannan ƙari da ake samu ta hanyar tsaurara sharuɗɗa ga masu neman takardar shiga ƙasar.

Elizabeth Ademuyi Anuoluwapo
Bayanan hoto, Elizabeth Ademuyi Anuoluwapo na ganin cewa idan mutum na son ya samu walwala dole ne ya fice daga Najeriya

Amurka da Canada ma wasu ƙasashe ne da ƴan Najeriyar ke son zuwa.

Elizabeth Ademuyi Anuoluwapo, wata ɗaliba ce a Najeriya wadda ke karatun harkar gidan namun daji, ta bayyana cewa fita zuwa ƙasashen ƙetare abu ne mai wahala, amma tana ganin cewa kamar hakan ne hanya ɗaya tilo ta samu isassun kuɗin da mutum zai dogara da kansa.

Lamarin ficewar ƴan Najeriya zuwa ƙasashen ƙetare ya shafi ɓangaren lafiya na ƙasar sosai.

A 2022 Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya ta ce aƙalla likitoci 50 na barin Najeriya a kowane mako.

Wannan ya sanya ɓangaren lafiya na ƙasar ya shiga mawuyacin hali.

Abubuwan da za su sa matasa su tsaya Najeriya

Wasu, kamar Dakta Vongdip Nankpah na Asibitin Koyarwa na Jami'ar Abuja na ganin cewa tsayawa gida abu ne mai muhimmanci.

Yana ganin cewa cimma buri a ɓangaren da mutum ya ƙware ya fi muhimmanci kan cimma buri na ƙashin kai - abu ne da ya shafi al'umma ba ki ɗaya da kuma irin gudumawar da mutum zai bai wa al'ummarsa.

Ya ce "idan ina na cimma abubuwa da dama a ɓangaren sana'ata, to gara na tsaya a Najeriya domin lalubo hanyoyin da za mu gyara ƙasar".

"Akwai dalilai da dama wadanda ke sa nake jin cewa gara mutum ya tsaya a ƙasarsa."

Amma duk da irin soyayyar da yake wa ƙasarsa, matashi Mista Olanrewaju na ganin cewa bai ci amanar ƙasarsa ba idan ya bar ta a yau, kuma ba zai yi nadamar hakan ba.

Ya ce "ni na yi fadi tashi wajen samun kusan duk abubuwan da na samu a rayuwa."

Yana ganin cewa shi zai zamo wakilin ƴan Najeriya ne a wata ƙasa.

Kamar wasu ƴan Najeriya da dama, yanzu haka Olanrewaju na ƙoƙarin kwatanta alfanun da zai samu idan ya fita waje da kuma kuɗaɗen da zai kashe a ƙoƙarin hakan.

Waɗanda suka taimaka wajen haɗa wannan labari: Makuochi Okafor, Faith Oshoko, Emily Horler da Alex Rhodes.