Me zai biyo bayan fitar da bayanan ƴan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da INEC ta yi?

Asalin hoton, Bola Tinubu/Peter Obi/Atiku Abubakar/Omoyele Sowore
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fara wallafa bayanai da takardun shaidar 'yan takarar shugaban ƙasa da jam'iyyun siyasa suka tsayar domin fafatawa a babban zaɓen shekarar 2027.
INEC ta ce matakin ya yi daidai da tanadin Dokar Zaɓe ta 2026 da kuma jadawalin zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa ta fara nuna bayanan ne a hedikwatarta da ke Abuja da kuma ofisoshinta da ke ƙananan hukumomin Babban Birnin Tarayya domin jama'a su duba su.
Jam'iyyun siyasa da suka hada da APC, ADC, Labour Party da wasu jam'iyyu sun riga sun miƙa sunaye da takardun 'yan takararsu ga INEC.
Hukumar ta ce manufar fitar da bayanan ita ce tabbatar da gaskiya da buɗaɗɗen tsari, tare da bai wa jama'a damar bincika cancanta da sauran bayanan da 'yan takaran suka gabatar.
Bisa jadawalin INEC, bayan karɓar fom ɗin tsayar da takara daga jam'iyyu, mataki na gaba shi ne wallafa bayanan 'yan takaran.
Hukumar ta riga ta wallafa sunayen 'yan takarar shugaban ƙasa da na majalisun dokoki a ranar 1 ga Agustan 2026, yayin da ake sa ran za ta fitar da sunayen 'yan takarar gwamna da na majalisun jihohi a ranar 29 ga Agustan 2026.
Wannan zai ba jama'a damar duba takardun da 'yan takaran suka gabatar kafin zaɓen 2027.
Waɗanne 'yan takara ne INEC ta wallafa bayanansu?
Kwamishinan zaɓe na Babban Birnin Tarayya (FCT), ya ce wallafa bayanan 'yan takara wani tanadi ne da ke cikin Sashe na 29(3) na dokar zaɓe ta 2026, wanda ya wajabta wa INEC nuna bayanai da takardun shaida na 'yan takara ga jama'a.
A cewar hukumar, fitar da bayanan ya shafi 'yan takarar shugaban ƙasa da kuma 'yan takarar Majalisar Tarayya da za su fafata a zaɓe a Babban Birnin Tarayya Abuja.
INEC ta ce wannan mataki wani muhimmin ɓangare ne na tsarin zaɓe domin ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da kuma ƙara yarda da yadda ake gudanar da zaɓe.
Kwamishinan ya kuma buƙaci jama'a su duba bayanan da kyau domin tantance takardu da sauran bayanan da 'yan takaran suka gabatar.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da bin jadawalin zaɓen 2027 tare da tabbatar da gudanar da zaɓe cikin adalci, gaskiya da sahihanci.
Mene ne mataki na gaba bayan INEC ta wallafa sunayen 'yan takara?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan wallafa bayanan da takardun shaidar 'yan takarar zaɓen 2027, jam'iyyun siyasa za su iya fara yaƙin neman zaɓe domin neman goyon bayan masu kaɗa ƙuri'a kafin gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa, majalisun tarayya, gwamnoni da majalisun dokokin jihohi.
Duk da haka, jadawalin INEC ya ba jam'iyyun siyasa damar janye ko maye gurbin wasu daga cikin 'yan takararsu idan buƙatar hakan ta taso.
Bisa tanadin Sashe na 31 na Dokar Zaɓe ta 2026, dole ne a yi hakan ƙasa da kwanaki 90 kafin ranar zaɓe.
Jam'iyyun siyasa na da wa'adin zuwa ranar 22 ga Agusta domin janye ko sauya 'yan takarar kujerun tarayya, yayin da wa'adin kujerun jihohi zai ƙare ne a ranar 19 ga Satumba.
Bayan kammala waɗannan matakai, INEC za ta sake wallafa jerin sunayen ƙarshe na 'yan takara da jam'iyyunsu aƙalla kwanaki 60 kafin zaɓe.
Wannan jerin sunayen ne zai zama na ƙarshe, ba tare da ƙarin sauye-sauye ba, yayin da jam'iyyu za su ci gaba da gudanar da yaƙin neman zaɓe har zuwa lokacin zaɓen.






