BBC ta gano sabbin ɓarnar da Iran ta yi wa sansanonin Amurka da muhimman wurare a yankin Gulf

..
    • Marubuci, Ahmed Nour, Sherihan Al-Akhras, and Mark Ellison
    • Aiko rahoto daga, BBC Fact Check
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Wani bincike na BBC ya gano sabbin ɓarnar da hare-haren Iran suka yi wa sansanonin sojin Amurka da muhimman wuraren fararen hula a wasu ƙasashen Larabawa, duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce an lalata ƙarfin sojin Tehran.

Sashen BBC Verify mai bincike ya tattara shaidu da ke nuna ɓarna a aƙalla sansanonin soja da muhimman cibiyoyi guda tara a Kuwait, Bahrain, Iraki da Jordan tun bayan fara sabon rikicin da ya ɓarke a ranar 12 ga Yulin 2026.

Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna cewa an samu sabbin ɓarnace-ɓarnace a ranar 12 ga Yuli da kuma bayan wannan rana, duk kuwa da cewa Shugaba Trump ya bayyana a watan Yunin 2026 cewa an "lalata" ƙarfin sojin Iran.

BBC ta kwatanta hujjojin da aka samu daga hotunan tauraron dan'adam da bidiyoyin da ta tabbatar da ingancinsu tare da waɗanda ta samu, sannan ta yi nazarin bayanan ikirarin da mahukuntan Iran suka yi.

Sakamakon binciken ya nuna cewa Iran har yanzu tana da wani ɓangare na ƙarfin da zai ba ta damar kai hare-hare kan sansanonin Amurka da muhimman cibiyoyi a faɗin yankin tun bayan fara sabon rikicin.

Har ila yau, BBC Verify ta gano wasu bidiyoyi na yaudara da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta da ke ikirarin nuna hare-haren Iran a ƙasashen Larabawa. Binciken ya nuna cewa wasu daga cikin bidiyoyin tsofaffi ne ko kuma an ƙirƙire su ne domin yaudarar jama'a.

Sakamakon binciken ya nuna ci gaba da barazanar da hare-haren Iran ke haifarwa a yankin, tare da ƙalubalen yaɗuwar bayanan ƙarya da ke tattare da rikicin.

Sabbin hare-haren sama kan sansanin soja a Jordan

..

Wasu daga cikin hujjojin da suka fi ƙarfi sun fito ne daga sansanin jiragen sama na Muwaffaq Salti, wani sansanin soja da ke yankin hamada a ƙasar Jordan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An kashe fiye da dala miliyan 140 na tallafin Amurka, kwatankwacin fam miliyan 104, wajen ayyukan bunƙasa sansanin. Haka kuma, rundunar sojin Amurka ta yi amfani da sansanin, kamar yadda cibiyar bincike ta Atlantic Council ta bayyana.

BBC ta tabbatar tun a watan Maris na shekarar 2026 cewa an lalata na'urar radar ta AN/TPY-2 da ke wurin. Wannan radar wani muhimmin ɓangare ne na tsarin kariyar makamai masu linzami na Amurka mai suna THAAD, wanda aka kera domin gano da kuma bibiyar makamai masu linzami.

Dakarun kare juyin-juya halin Iran, sun ce hare-haren da suka kai a watan Yuli sun lalata wurare sama da 20 a sansanin.

BBC ba ta tabbatar da adadin da dakarun na Iran suka bayyana ba, amma kwatanta hotunan tauraron dan'adam da aka ɗauka kafin harin da bayan harin ya tabbatar da cewa an sake kai hari kan sansanin a tsakiyar watan Yuli.

Hotunan sun nuna lalacewar wani wurin da ake zargin mafakar jiragen sama marasa matuƙi ce da kuma tankunan jiragen sama da dama. Haka kuma, an ga wasu gine-gine da kayayyakin aiki a wasu sassan sansanin sun ƙone sakamakon harin.

Barnar da ta auku a sansanin Tower 22

..

Hotunan tauraron ɗan'adam da aka ɗauka kafin harin da kuma bayan harin sun nuna abin da ake ganin lalacewa ce a sansanin Tower 22, wani wurin sojin Amurka da ke Jordan kusa da iyakokin Siriya da Iraki.

Sabbin hotunan sun nuna cewa wurin ya sake fuskantar ƙarin barna. Sai dai har yanzu ba a tantance girman ɓarnar ba, ko kuma irin tasirin da ta yi wa ayyukan sansanin.

A watan Janairun 2024, sojojin Amurka uku sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan wani jirgi maras matuƙi ya kai hari kan sansanin.

Ɓarnar da aka samu a cikin wani sansanin soja a Bahrain

..

BBC ta gano shaidun lalacewa a sansanin jiragen sama na Sheikh Isa da ke Bahrain, inda sojojin Amurka ke da matsuguni.

Hotunan tauraron ɗan'adam da aka ɗauka bayan harin, wanda Iran ta ɗauki alhakinsa, sun nuna lalacewar wani gini da ke cikin sansanin.

Gwamnatin Bahrain ta yi Ala-wadai da harin da Iran ta kai, tana mai cewa a cikin wata sanarwa cewa Iran, ta hanyar wannan hari, na ci gaba da nuna "halayyarta ta ƙiyayya mai tsari", wadda ta ce tana dogaro ne da "munanan hare-hare da ke kai wa fararen hula hari a Masarautar Bahrain."

Lalata wasu kayayyaki da gine-gine a sansanin jiragen sama na Erbil

..

A gefe guda kuma, a sansanin jiragen sama na Erbil da ke arewacin Iraki, hotunan tauraron ɗan'adam da sashen BBC Verify ya binciko sun nuna shaidun cewa an kai hari a wurin.

Kwatanta hotunan da aka ɗauka kafin harin da kuma bayan harin ya nuna cewa an lalata wasu ƙananan gine-gine da kayayyaki a cikin sansanin. Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da takamaiman amfanin waɗannan wurare ba.

Erbil na daga cikin wuraren da suka sha hare-haren jirage marasa matuƙa tun bayan da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ya sake ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya.

Gobara ta tashi a wata babbar matatar mai a Kuwait

..

A Kuwait kuwa, hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna lalacewa a matatar mai ta Mina Abdullah, wadda ke daga cikin muhimman cibiyoyin masana'antar mai ta ƙasar, tsakanin ranar 13 zuwa 23 ga watan Yuli.

Kai hare-haren kan wannan matata na nuna yadda hare-haren suka faɗaɗa daga sansanonin soja masu alaƙa da Amurka zuwa muhimman cibiyoyin makamashi. Wannan na iya zama barazana ga samar da mai da kuma wadatar makamashi a yankin.

Kamfanonin Amurka masu samar da hotunan tauraron ɗan'adam sun sanya wasu takunkumai kan hotunan Iran da maƙwabtan ƙasarta jim kaɗan bayan ɓarkewar yakin.

Saboda haka, sashen BBC Verify ya yi amfani da nau'o'in hujjojin gani daban-daban wajen tantance girman lalacewar, ciki har da bidiyoyi da hotunan tauraron ɗan'adam na Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Turai (ESA).

Bidiyoyi sun kuma nuna wasu abubuwa uku da suka faru a Kuwait, amma har yanzu ba a sami hotunan tauraron ɗan'adam da suka tabbatar da su ba.

Wani bidiyo da BBC ta tantance wurin da aka ɗauke shi ya nuna abin da ya yi kama da hari kan wani sito a ranar 15 ga Yuli.

Wani bidiyon kuma ya nuna yiwuwar harin da aka kai kan wani tsohon sansanin Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar 12 ga Yuli.

Sai wani bidiyo na uku da aka ɗauka a ranar 18 ga Yuli, wanda ya nuna wani hayaki da ya turnuƙe mai yawa yana tashi daga unguwar Fahad Al-Ahmad da ke kudancin birnin Kuwait.

Me shaidun ke nunawa?

Hotunan tauraron ɗan'adam da bidiyoyin da BBC ta tabbatar da sahihancinsu sun nuna cewa an kai hare-hare kan sansanonin soja da muhimman cibiyoyi a ƙasashe huɗu tun daga ranar 12 ga Yuli da kuma bayan wannan rana.

Har yanzu ba a tantance cikakken tasirin wasu daga cikin barnar da aka samu kan ayyukan waɗannan wurare ba.

Duk da haka, lalacewar sansanonin soja, hare-haren da suka shafi wuraren da ke da alaƙa da Amurka, da kuma gobarar da ta tashi a wata babbar matatar mai suna nuna cewa muhimman wurare a yankin Gulf da Jordan har yanzu na cikin haɗarin hare-hare.

Hakan na zuwa ne duk da sanarwar da Washington ta yi a watan Yuni cewa ta yi nasarar karya ƙarfin sojin Iran.

Tun bayan ɓarkewar yaƙin, Iran da ƙungiyoyin da ke da alaƙa da ita sun kai daruruwan hare-hare a ƙasashen Larabawa ta amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

Hare-haren sun shafi sansanonin soja da muhimman cibiyoyin more rayuwa, kuma tasirinsu ya kai har zuwa wuraren da fararen hula ke rayuwa a faɗin yankin.

A ranar 25 ga Yuli, ƙungiyar Houthi ta Yemen mai samun goyon bayan Iran ta kai hari kan cibiyoyin man fetur na Saudiyya a tashoshin jiragen ruwa biyu da ke gaɓar Tekun Red Sea.

Kakakin sojin Houthis, Yahya Saree, ya ce ƙungiyar ta kai hari kan wuraren kamfanin Saudi Aramco da ke Jazan da Yanbu.

A Masar kuma, Majalisar Ministoci ta sanar da cewa wani jirgi maras matuƙi ne ya haddasa gobara a wasu tankokin iskar gas guda biyu a tashar jiragen ruwa ta Damietta. Gwamnatin ta jaddada cewa lamarin hari ne da aka kai, ba hatsari ba ne.