A wajenmu, duk wata barazana muna ɗaukarta da gaske - Iran

Asalin hoton, Getty Images
Iran ta ce tana ɗaukar duk wata barazana da ake yi mata a matsayin ta gaske kuma mai muhimmanci, duk kuwa da cewa wasu daga cikinsu na iya kasancewa wani ɓangare na yaɗa tsoro.
Mukaddashin Ministan Tsaron Iran, Majid Ibn Reza, ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce daga babu wata barazana da Iran za ta yi watsi da ita ko a ɗauka da wasa.
Ya ƙara da cewa Iran ba ta mamakin irin waɗannan barazanar kuma ba ta zama cikin sakaci, sai dai tana amfani da su wajen ƙara ƙarfafa shirinta na tsaro, da matakan kariya da kuma ƙarfin daƙile hare-hare.
Kalaman nasa na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya dakatar da shirin kai hari kan Iran a halin yanzu, bayan buƙatun da Iran da wasu ƙasashen yankin suka yi domin ba da damar warware rikicin ta hanyar tattaunawa.
























