Manyan cutuka biyu da ke hana mata haihuwa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Aisha Shariff Baffa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Cutar PCOs, wadda a yanzu aka sauyawa suna zuwa PMOS (Polyendocrine Metabolic Ovarian Syndrome), cuta ce wadda ke shafar ƙwayayen mahaifa da rikicewar sinadaran hormone, kuma cuta ce da ke shafar mata musamman waɗanda suka kai shekarun haihuwa.
Cutar na faruwa ne lokacin da aka samu rashin daidaiton sinadaran hormone a jikin mace, wanda kan hana ƙwai yin girma da fitowa yadda ya kamata.
Ana samun cutar ne daga inda mace ke fitar da ƙwanta.
Ita kuwa cutar fibroid cuta ce da wasu ke kiranta da cutar kwanci.
Wato wani tsiro ne da ke fitowa a cikin mahaifar mace sai ya riƙa girma har ya kai mizanin da zai iya haifar da wasu matsaloli.
Mene ne ya bambanta PMOS da Fibroids?
Dr Bilal Suleiman, kwararren likitan mata ne da ke aiki a asibitin koyarwa na jami'ar Abuja da ke Gwagwalada, ya ce akwai abubuwa da dama da suka bambanta waɗannan cutuka:
- -Na farko, ita PMOS a cuta ce da ke shafar kwayayen mahaifa, yayin da ita kuma Fibroids cuta ce da ke fitowa a cikin mahaifa.
- -Na biyu kuma in ji likitan shi ne, sinadarin da ke da dangantaka da cutar fibroids ana kiransa da estrogen, wato sinadari ne wadanda mafi yawancin mata ke da su, kuma yana taimakawa mace ta zama cikakkiyar mace. Idan sinadarin ya yi yawa yana haddasa toho a cikin mahaifa. Ita kuwa cutar PCOs sinadarin da ke dan dangantaka da ita shi ne androgene. Ma'ana sinadaran da ke tattare da waɗannan cutuka sun bambanta su.
- -Bambanci na uku da ya bambanta waɗannan cutuka, shi ne a wajen jinin al'ada da mata ke yi, idan mace na dauke da cutar fibroids za ta ga tana zubar da jini mai yawa wani lokaci ma har da guda-guda, sannan kwanakin yin al'adar na ƙaruwa, ga mace mai ɗauke da cutar PCOs kuwa, al'adarta wasa ta ke yi, ma'ana ta zo yau gobe kuma ta ɗauke ko kuma idan ta zo wannan makon ta ɗauke, sai bayan mako biyu kuma sai ta dawo.
Wani lokaci ma mai fama da wannan cuta kan shafe wata biyu zuwa uku ba ta yi al'ada ba, akasin mai fibroids da a kowanne wata sai ta yi jini al'ada.
Likitan, ya ce a wasu lokuta mace mai cutar PCOs idan ta tashi al'ada ita ma musamman idan ta shafe wata biyu zuwa uku bata yi ba, jinin na zuba da yawa da har a wasu lokuta ma akan ƙara mata jini.To amma shi fibroids bai cika zuwa da ɗaukewar jini ba.
Ya ce," Idan mace na da cutar PCOs saboda ta kan shafe wata biyu zuwa uku ba ta ga jinin al'adarta ba, wani lokaci sai tayi zaton ma ko juna biyu gareta.
Likitan ya ce wani abu kuma da ya bambanta waɗannan cutuka shi ne, ga mai ɗauke da cutar fibroids, idan ya girma sosai yana iya danne mafitsara, ko kuma danne bututun da ya hade da dubura
A cewarsa, hakan kan sa idan mace za ta yi fitsari muddin ya kai wannan matakin, za ta ji tana jin ciwo, ko kuma ta rinƙa fitsarin kaɗan-kaɗan, haka ma idan ta je yin bayan gida saboda tsiron ya danne bututun da ya haɗe da dubura, sai ta kasa yin bayan gidan sai da ƙyar, to amma shi PCOs, da ya ke ba tsiro ba ne baya jan waɗannan matsalar saboda shi ya fi shafar sinadarai.
Kamanceceniyar da ke tsakanin PMOS da Fibroids
Dr Bilal Suleiman, ya ce akwai wasu abubuwa da suka waɗannan cutuka ke da dangantaka ko kuma kamaceceniya.
Na farko ya ce, "dukkan waɗannan cutuka na da dangantaka da matsalar haihuwa, ma'ana rashin haihuwa, kodaya ke ya ce shi fibroids bai da alaƙa da rashin haihuwa kai tsaye."
To amma a mafi yawancin lokuta idan ya yi girma sosai a cikin mahaifar mace jariri bai zai iya zama a ciki ba, sannan kuma wani lokacin bututun da zai ɗauki maniyin namiji ya kai kwan mace ya ke su haɗu fibroids ɗin na iya toshe shi.
Hakan zai sa mace ta kasa samun juna biyu.

Asalin hoton, Getty Images
Shi kuwa PCOs, in ji likitan, cuta ce da ke da dangantaka da inda mace ke fitar da kwai, dan haka ba zata iya fitar da ƙwai ba kafin ta yi al'ada, a ka'aida a duk wata mace na fitar ƙwai ɗaya, to mace mai PCOs ba ta ma fitar da shi, ballanatan ta ɗauki ciki.
Likitan matan, ya ce wani abu da ya dangantaka waɗannan cutuka kuma shi ne zubar da jini mai yawa musamman a lokacin al'ada.Ya ce dukkansu suna haddasa mace ta zubar da jini fiye da ƙima inda a wasu lokuta ma akan kai ga ƙarin jini.
Dr Bilal, ya kuma dukkan cutukan ba su da alaƙa da cutar kansa ta mahaifa, sannan kuma kwai wasu magunguna da ake amfani da su wajen dakatar da zubar jini ga masu waɗannan cutuka, maganin irin ɗaya ne.
Mene ne alamomin waɗannan cutuka?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dr Bilal, ya ce fibroids za ka ga mata da yawa suna da shi amma ba su san suna da shi ba saboda ƙila ƙarami ne sosai ba kuma ya bayar da wata matsala, to amma idan har ya fara girma ko kuma mace ta fara fuskantar wasu alamomi a jikinta ta je asibiti aka duba anan za a gano tana da shi.
Ya ce," Daga cikin alamomin da mace za ta lura da su shi ne za ta ga ƙasan cikinta ma'ana mararta ta ɗan kumbura wanda idan aka taɓa za a ji yana da karfi ko tauri, kuma idan aka taɓa shi baya ciwo, sannan kuma idan ya girma sosai yana haddasa zubar jini sosai a lokacin al'ada.
Sannan yana iya hana haihuwa ko zubar ciki ɓari ke nan. Kuma idan fibroids ya yi girma sosai zai iya danne mafitsarar mace ta kasa yin fitsari ko kuma ta rinƙa yinsa da ƙyar koma ta kasa riƙe fitsari.Sai kuma ciwon mara idan ya yi girma sosai."
Ga mace mai PCOs kuwa, alamoninsa, in ji likitan sun haɗa da rashin haihuwa da ɗaukewar al'ada, ma'ana mace ta shafe watanni ba tare da taga al'adarta ba, ga kuma zubar da jini da yawa a lokacin al'ada.
Dr Bilal, ya ce, sauran alamomin PCOs sun haɗar da fitowar ƙuraje a jiki musamman a fuska, sannan akwai fitowa gashi kamar na maza ga mace mai cutar PCOs, za ta ga gashin baki ko gemu na fito matakai har ma da fitowar gashi ƙirjinsu ko kuma su ga gashin gabansu ya yi yawan da ya kai kusa da cibiyarsu.
Sannan ga zau rinƙa yawan fuskantar ɓacin rai, ga kuma yawan zufa a lokutan da ba su kamata ba ace sun yi zufar ba, idan ya tsananta ma muryarsu ma na iya canzawa ta koma kamar ta maza.

Asalin hoton, Getty Images
Likitan ya ce, kuma mafi yawanci mata masu ƙiba sun fi kamuwa da cutar PCOs, shi ya sa sau da dama in ji ake shawartar matan da ke da shi ciwon idan suna da ƙiba da su sauya yanayin rayuwarsu ta fuskar abinci da motsa jiki, saboda koda an ba su magani ya yi aiki.
Likitan matan ya ce, ga mace mai cutar fibroids tana iya warkewa, saboda tsiro ne idan aka cire shi shi ke na, amma mai cutar PCOs, ba a warkewa kamar ciwon siga ne sai da a bayar da magani, shi ma haka ya ke saboda abin ya shafi sinadarai, sai dai a bayar da magungunan da za su rage tsananin alamunsa.










