'Jihohin Najeriya 8 da za su fuskanci ambaliya cikin watan Agusta'

Ambaliya ruwa

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Yayin da damina ke ƙara tsananta a sassa da dama na Najeriya, Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Ƙasa (NIHSA) ta sake yin gargaɗin yiwuwar ambaliya a wasu jihohin ƙasar cikin watan Agusta.

Hukumar, a cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, ta lissafo wasu jihohi da take ganin suna cikin haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa, lamarin da ka iya haddasa asarar dukiyoyi tare da tarwatsa harkokin rayuwar jama'a.

Galibi watan Agusta an fi fuskantar wayan mamakon ruwan sama a wasu yankunan Najeriya, lamarin da ya sa ambaliya ta fi ƙamari a watan.

NIHSA ta ce ambaliyar za ta shafi makarantu da kasuwanni da wuraren ibada a garuruwa masu yawa na jihohin da ta hukumar ta lissafo.

A kowace shekara ambaliya ta ruwa kan janyo mummunar ɓarna a Najeriya, inda take haifar da asarar rayuka da dukiyoyi a ƙasar.

Bisa bayanan na hukumar ta NIHSA , mun duba wasu jihohin ƙasar shida da ta ce za a fi samun haɗarin ambaliyar da kuma matakan da ya kamata mazauna wuraren su ɗauka domin rage hatsarin.

Kaduna

Ambaliya

Asalin hoton, Getty Images

Jihar Kaduna da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na cikin jihohin da hukumar ta ce suna cikin hatsarin fuskantar ambaliyar.

A cewar hukumar ta NIHSA ƙananan hukumomin jihar takwas ne ke cikin fuskantar ambaliyar a watan na Agusta.

Ƙananan hukumomin jihar da ke cikin wannan hatsari sun haɗa da Igabi da Jema'a da Kajuru da Ƙaura da Sanga da Soba da Zangon Katab da sauransu.

Hukumar ta ce gauruwa da ƙauyukan jihar fiye da 300 ne ke cikin hatsarin ambaliyar, yayin da makarantu fiye da 90 da wuraren ibada fiye da 50 ke cikin barazanar ambaliyar.

Neja

Ambaliya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A shekarar 2025 ne Neja ta fuskanci wata mummunar ambaliyar da ta kashe fiye da mutum 200 a jihar.

Jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya na cikin jihohin da hukumar NIHSA ta lissafa cikin jihohin da ke fuskantar hatsarin ambaliya a cikin watan na Agusta mai kamawa.

NIHSA ta ce ƙananan hukumomin jihar 16 ne ke cikin hatsarin fuskantar bala'in.

Wasu daga cikin ƙananan hukumomin sun haɗa da Agaie da Boss0 da Edati da Gbako da Gurara da Lapai da sauransu.

Hukumar ta ce garuruwa da ƙauyukan jihar kusan 700 ne ke cikin hatsarin ambaliyar.

NIHSA ta ce makarantu fiye da 330 da kasuwanni 14 da wuraren ibada fiye da 200 da kuma cibiyoyin lafiya fiye da 170 ne ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar.

A farkon shekarar 2025 ne wata mummunan ambaliya da ta auka wa jihar Neja ta kashe fiye da mutum 200.

Filato

Ita ma jihar Filato mai maƙwabtaka da Neja ta shiga jerin jihohin da hukumar ta yi wa gargaɗin fuskantar ambaliya cikin watan na Agusta.

NIHSA ta ce ƙananan hukumomin jihar takwas ne ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar.

''Ambaliyar za ta shafi garuruwa da ƙauyukan jihar fiye da 200'', a cewar hukumar.

Hukumar kula da harkokin ruwan ta Najeriya ta ce ambaliyar za ta shafi makarantu fiye da 100 da kasuwanni ko wuraren sana'a fiye da 20 da cibiyoyin lafiya fiye da 80 a faɗin jihar.

Ambaliya

Asalin hoton, Getty Images

Bauchi

Jihar Bauchi ta shiga jerin jihohin da suka samu gargaɗin ambaliyar daga hukumar kula da harkokin ruwan ta Najeriya.

Hukumar ta NIHSA ta ce ƙananan hukukomin Bauchi biyar ne ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar da suka haɗa da Alƙaleri da Gamjuwa da Kirfi da Bauchi da kuma Tafawa Balewa.

A cewar hukumar garuruwa da ƙauyukan jihar fiye da 700 ne ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar.

NIHSA ta ce makarantun jihar Bauchi fiye da 150 da cibiyoyin lafiya fioye da 50 da wuraren ibada fiye da 160 ne ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar.

Gombe

Ambaliya

Asalin hoton, Getty Images

Jihar Gombe mai maƙwabtaka da Bauchi na cikin wannan jeri a cewar hukumar kula da harkokin ruwan ta Najeriya.

A cewar hukumar ƙananan gauruwa da ƙauyukan jihar kusan 200 ke cikin barazanar ambaliyar a cikin watan na Agusta.

NIHSA ta ce ambaliyar na barazana ga makarantun jihar fiye da 70 da wuraren ibda fiye da 50 sai kuma cibiyoyin lafiya fiye da 40.

Taraba

Ambaliya

Asalin hoton, Getty Images

Jihar Taraba da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya na cikin jihohin ƙasar da NIHSA ta ce suna cikin hatsarin fuskantar ambaliya a Najeriya cikin watan na Agusta.

Hukumar ta ce jihar Taraba - wadda ta yi iyaka da kasar Kamaru - kan fuskanci ambaliya a wasu lokutan.

''Ƙananan hukumomin jihar takwas ne ke cikin hatsarin fuskantar ambaliya a watan na Agusta'', in ji NIHSA.

A bayanin gargaɗin da hukumar ta fitar ta ce makarantu fiye da 200 da cibiyoyin lafiya fiye da 100 da kuma wuraren ibada fiye da 90 ne ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar.

Ambaliya

Asalin hoton, Getty Images

Benue

Jihar Benue mai albarkar ƙasar noma a Najeriyar na cikin jihohin ƙasar da za su iya fukantar ambaliya cikin watan na Agusta.

NIHSA ta ce ƙananan hukumomin jihar 10 ne cikin hatsarin fuskantar wannan matsala.

Hukumar ta ce ambaliyar za ta iya shafar garuruwa da ƙauyukan jihar kusan 300 ne ke cikin wannan hatsari na ambaliya.

A cewar NIHSA makarantun jihar fiye da makarantun jihar fiye da 200 da cibiyoyin lafiya fiye da 130 da wuraren ibada fiye da 270 ne ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar.

Legas

Ambaliya

Asalin hoton, Getty Images

Jihar Legas da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya ta kasance kan gaba wajen samun aukuwar ambaliya a yakin musamman a wannan shekara.

Hukumar ta NIHSa ta ce ƙananan hukumomin jihar bakwai ne ke cikin hatsarin fusknaytar ambaliyar.

Waɗanda suka haɗa da: Lekki/Ijebu da Badagary da Epe Eti-Osa da Ikorodu da Lagos Island da Ojo.

A duk lokacin da jihar Legas ta fuskanci Ambaliya, yakan haifar da mummunar illa, lamarin da masana ke alaƙanta shi da yadda jihar ke kewaye da ruwa.

NIHSA ta ce garuruwa da unguwannin Legas fiye da 250 ne cikin hatsarin fukantar ambaliyar, lamarin da hukumar ta ce zai shafi makarantun jihar fiye da 400 da kasuwanni 41 da cibiyoyin lafiya fiye da 120 da wuraren ibada fiye da 100.

Sauran jihohin sun haɗa da:

  • Ogun
  • Kogi
  • Bayelsa
  • Imo da Anambra
  • Akwa Ibom
  • Edo
  • Abuja
  • Enugu
  • Ekiti
  • Ebonyi
  • Cross-River

Matakan da ya kamata a ɗauka

Hukumar ta kuma bayyana jerin matakan kariya da suke shawarci mutane yankunan su ɗauka domin kaucewa ko rage hatsarin ambaliyar.

Matakin da NIHSA ta lissafo sun haɗa da:

  • Kafa runduna ko tawagar masu aikin ceto ta masu jiran ko-ta-kwana.
  • Tanadar kayayyakin agaji da kayan aikin ceto.
  • A guji tsallaka titunan da ambaliyar ta cinye su da ƙafa ko abin hawa.
  • A kauce wa tsallaka ruwan da ke tsaka da gudu da ƙafa ko abin hawa.
  • Share magudanar ruwa ta yadda ruwa zai riƙa wucewa cikin sauƙi.
  • Kauce wa yin gini kan hanyoyin ruwa.
  • Ƙaurace wa gauruwa da ƙauyukan da hukumar ta ce suna fuskantar ambaliyar.
  • Yawaitar ziyartar shafin hukumar NIHSA domin domin samun bayanan da take fitarwa a kai-akai.