Abin da muka sani kan harbe-harbe a babban filin jirgin saman Nijar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Rahotanni na cewa dakarun jamhuriyar Nijar sun ce sun yi nasarar daƙile wani harin da aka kai da sanyin safiyar ranar Alhamis a filin jirgin saman Diori Hamani da ke Yamai, babban birnin ƙasar.

Kawo yanzu babu wasu cikakkun bayyanai ko sanarwa da suka fito daga hukumomin ƙasar game da wannan hari wanda shi ne na biyu a ƙasa da watanni 6 a filin jirgin na Yamai.

Sai dai rahotanni sun ce an tsaurara matakan tsaro inda Jami'ai suka killace kewayen filin jirgin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike a manyan tituna.

Tuni dakarun ƙasar suka fara farautar mutanen da ake zargi da kai hare-haren inda wasu bidiyo da suka rinƙa yawo suka nuna yadda aka harbe wasu da ke sanye da kakin soji ɗauke da makamai.

Da safiyar ranar Alhamis ɗin ne dai mazauna Yamai, babban birnin Nijar din suka bayyana jin ƙarar harbe-harbe a babban filin jirgin saman birnin.

Lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 6:00 na safe agogon ƙasar, kmar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato, yana mai cewa an shafe kusan sa'a guda ana jin ƙasar.

An jin ƙarar harbe-harben daga ƙofar shiga filin jirgin, kamar yadda wasu shaidu biyu suka bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Jamhuriyar Nijar ta shafe fiye da shekara 10 tana fama da matsalar masu iƙirarin jihadi da ke kai hare-hare kan hukumomin ƙasar.

Ko a watan Janairun wannan shekara ma masu iƙirarin jihadi sun kai wani harin a filin jirgin saman na Yamai, wanda ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kai shi.

Kamar dai sauran makwabtanta Burkina Faso da Mali, Nijar na ƙarƙashin mulkin soji.

A ranar 28 ga watan Janairun 2026 ɗin nan ma an samu harbe-harbe da fashe-fashe a kusa da babban filin jirgin sama na Diori Hamari da ke babban birnin na Niamey na Jamhuriyar Nijar.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da aukuwar lamarin, sannan wasu faye-fayen bidiyo sun bayyana yadda wasu na'urorin kariya na sararin samaniya ke ta ƙoƙarin tare wasu abubuwa da ba a iya tantancewa da tsakar dare.

Daga baya dai komai ya lafa, kamar yadda aka ruwaito daga wani jami'in gwamnati, duk da cewa bai yi ƙarin haske ba kan lamarin ba.

Jamhuriyar Nijar dai tana fama da ƙungiyoyi masu iƙrarin jihadi da ke addabar sassan ƙasar kamar Boko Haram da ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), mai alaƙa da Al-Qaeda.

A baya-bayan nan ne hukumomi a jamhuriyar ta Nijar suka ƙaddamar da wani aikin rushe gidaje fiye da 26,000 da ke kusa da filin jirgin saman na Diori Hammani da ke birnin Niamey.

Hukumomin dai sun ce sun ƙudiri niyyar rushe gidajen ne bisa dalilan tsaro, wani al'amari da ya janyo tankiya tsakaninsu da ƴan ƙasar musamman mutanen da abin ya shafa.