Me ya sa ake taƙaddama tsakanin Seyi Tinubu da 'shugaban ɗaliban' Najeriya?

Nigeria President Seyi Tinubu

Asalin hoton, Seyi Tinubu/Instagram

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ɗan shugaban Najeriya, Seyi Tinubu ya mayar da martani ga wani labari da ke cewa ya tura ƴan daba sun far wa shugaban wani ɓangare na Ƙungiyar Dalibai ta Najeriya (NANS), Atiku Isah.

Ɗan na shugaban Najeriya wanda ya musanta zargin a shafinsa na instagram a ranar Juma'a, ya ce zargin wani yunƙuri ne na shafa masa kashin kaji.

Ya ce: "...ta yaya mutum zai zabga ƙarya haka. Wannan wani yunƙuri ne na shafa min kashin kaji".

Ya kuma ce bai taɓa haɗuwa wanda ya yi zargin ba, wato Atiku Isah.

Martanin da ya mayar na zuwa ne bayan shugaban wani ɓari na Ƙungiyar ɗalibai ta Najeriya ya zargi Seyi Tinubu da ƙoƙarin bayar da cin hanci, da garkuwa da shi, da yi masa duka da wasu abubuwa da dama.

Seyi Tinubu Instagram story screen shot

Asalin hoton, Seyi Tinubu/X

A wani taron manema labarai da ya yi a baya-bayan nan, shugaban na ƙungiyar NANS, ya zargi ɗan shugaba Tinubu da tura ƴan daba waɗanda suka haifar da hatsaniya a inda ake rantsar da shi, wanda aka gudanar a Abuja, babban birnin ƙasar.

Ya kuma zargi ɗan shugaban ƙasar da yunƙurin ba shi cin hancin naira miliyan 100 domin mara wa Shugaba Tinubu baya, lamarin da ya ƙi amincewa da shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya yi zargin cewa sanadiyyar ƙin karɓar cin hancin ne wasu ƴan daba suka kama shi a ranar 15 ga watan Afrilu, inda suka yi masa duka.

A cikin bidiyon taron manema labaran da ya gabatar, Isah ya ce:

"Sun gayyace ni zuwa Legas domin haɗuwa da Seyi. Na gana da Seyi da kuma ministan matasa. A lokacin da na haɗu da ministan ya rungume ni sannan muka tattauna, sai suka so su ba ni naira miliyan 100, to amma ba komai ne za a mayar batun kuɗi ba.

"Ina da aƙiduna. Ba za ka tsammaci na fara koɗa shugaban ƙasar da bai tsinana min komai ba, in yi ƙaryar cewa ya yi. Idan ya yi abin kirki za mu faɗi kuma za mu goya masa baya, amma idan ya yi abin da ba daidai ba, ba za a ce mu rufe bakinmu ba, ba za mu yi haka ba."

Ya ƙara da cewa "sun kama ni a ranar 15 ga watan Afrilu, suka cire min kaya sannan suka min duka sosai. Suka kuma yi barazanar fitar da bidiyon dukan.

Hotunan dukan da Atiku Isah ya yi zargin an yi masa na ci gaba da yawo a shafukan sada zumunta, sai dai BBC ba ta iya tantance sahihancinsu ba.

Seyi, wanda ɗaya ne daga cikin ƴaƴan shugaban Najeriya Bola Tinubu ya daɗe yana haifar da cece-ku-ce a ƙasar sanadiyyar rawar da yake takawa a harkar siyasa da na shugabanci.

A baya-bayan wasu sun soke shi kan ran-gadin da ya yi a jihohi da dama na Najeriya, inda a wasu wurare ya riƙa raba abinci ga 'mabuƙata'.

Haka nan a farkon shugabancin Tinubu an soki yadda Seyi ke halartar zaman da mahaifinsa ke yi da manyan jami'an gwamnati.