An tsayar da ranar saurarar tuhumar Man City kan laifi sama da 100

Asalin hoton, Getty Images
Babban jami'in Premier League, Richard Masters ya ce an tsayar da ranar saurarar tuhumar Manchester City kan zargin karya dokar kasuwanci.
To sai dai kuma Masters bai fayyace ranar da za a fara saurarar tuhumar da ake yi wa kungiyar da ke Etihad ba.
Tuni aka kwashe maki 10 a Everton, bayan da aka samu kungiyar da laifin karya dokar kasuwanci kungiya, laifi iri daya da na Man City.
Ranar Litinin an tuhumi Nottingham Forest da laifin karya dokar cin riba a lik da kasa samar da bayanai kan dorewar kasuwancin kungiya.
Tun cikin Fabrairun 2023 ake tuhumar Manchester City da karya doka 100, wadda har yanzu ba a gurfanar da ita ba, don fuskantar hukunci.
A cikin watan Nuwamba aka yanke hukuncin cire maki 10 a Everton, bayan da a watan Maris kwamiti mai zaman kansa ya samu kungiyar Goodison Park da laifi.
Ana tuhumar Manchester City da aikata laifukan tun daga 2009, kuma tun daga lokacin kungiyar ta dauki manyan kofi bakwai.
Wasu na cewar watakila a kori Man City daga Premier League zuwa Championship da karbe kofunan da ta lashe, idan aka samu kungiyar da laifi.
Ana kuma tuhumar kungiyar da kin bayar da hadin kai tun daga lokacin da Premier League ta fara tuhumar Man City a 2018.
Wasu rahotanni na cewa watakila a fara sauraren tuhumar City a karshen shekarar 2024, amma ba a samu tabbaci ba daga mahukuntan Premier League ba.
Amma ana sa ran za a yanke hukunci kan Manchester City a 2025.











