Gane Mani Hanya tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Bayanan sautiLatsa sama don sauraron tattaunawar
An wallafa

Batun da yanzu haka yake ci gaba da yamutsa hazo a kafafen sada zumunta shi ne na murabus daga shugabancin hukumar Hizba ta Kano da Sheikh Aminu Daurawa ya yi a jiya Juma’a.

Da safiyar Juma’ar ne dai Sheikh Daurawa, a wani sakon bidiyo a shafinsa na Facebook, ya sanar da ajiye mukamin nasa wanda hakan ba ya rasa nasaba da wani jawabi da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi dangane da ayyukan rundunar ta Hizba.

To kafin dai wannan murabus, BBC ta tattauna da malam Aminu Daurawa dangane da ayyukan Hizbar da ma abubuwan da ake zargin dakarun hukumar da aikatawa.

A hirarsa da Madina Maishanu, Sheikh Daurawa ya fara da bayani kan ayyukan rundunar ta Hizba.