Gasar kofin duniya 2030: Kasashe 6 za su karbi bakuncin wasannin

World Cup

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Za a gudanar da gasar cin kofin duniya a 2030 a kasahe shida kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta sanar.

An bayyana Sifaniya da Portugal da Morocco cikin masu hadaka, yayin da za a fara wasa uku a Uruguay da Argentina da kuma Paraguay.

Wasan da za a fara a Kudancin Amurka a gasar zai zama na bikin shekara 100 da Fifa ta fara gabatar da gasar a Montevideo.

A shekara mai zuwa hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa za ta tabbatar da wannan tsarin a babban taron da za ta gudanar.

Fifa ta kara da cewar za ta duba damar bayar da karbar bakuncin gasar kofin duniya a 2034, tsakanin nahiyar Asia da yankin Oceania.

Ana sa ran Saudi Arabia za ta karbi bakuncin wasannin da za a yi a 2034 a karon farko a tarihi.

Birnin Montevideo a Uruguay shi ne ya karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a 1930, a nan za a buga wasan farko a 2030 daga nan a yi fafatawa a Argentina da kuma Paraguay.

Sauran wasannin daga fafatawa 48 za a raba tsakanin Afirka da Turai, wato Morocco da Portugal da Sifaniya.

Idan har an amince da wannan shirin, Morocco za ta zama ta biyu a Afrika da za ta karbi bakuncin gasar kofin duniya, bayan Afirka ta Kudu a 2010.

Portugal ba ta taba karbar bakuncin gasar kofin duniya ba, amma ta gudanar da wasannin cin kofin nahiyar Turai a 2004.

Sifaniya ta karbi bakuncin gasar 1982, inda Italiya ta lashe kofin na uku jimilla.

Qatar ce ta gudanar da gasar kofin duniya da aka yi a 2022, wadda Argentina ta dauka na uku a tarihi.