Me ya sa Wike ya zamar wa PDP ƙarfen ƙafa?

Asalin hoton, BBC Pidgin
Alamu na nuna cewa tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan babban birnin Najeriya, Abuja, Nyesom Wike na ci gaba da gagarabadau a jam'iyyar hamayya ta PDP.
Hakan ya biyo bayan barazanar hukunta Nyesom Wike da jam'iyyar ta yi a lokuta daban-daban bisa dalilan yi wa jam'iyyar ta PDP zagon ƙasa.
Wike ya sha faɗin cewa ya yi wa shugaba Tinubu aiki a zaɓen 2023, sannan kuma shi yake son ya sake cin zaɓe a 2027.
Abu 6 da Wike ya yi a PDP
- Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya sha iƙrarin cewa a 2023 shugaba Tinubu ya zaɓa kuma shi ɗin zai sake goyan baya. Duk da jam'iyyar ta ce za ta hukunta shi amma ba ta iya yin hakan ba.
- Wike ya tsaya kai da fata cewa idan dai ana son a samar da zaman lafiya a jam'iyyar ta PDP to dole ne a amince da ɗantakarsa, Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa. Kuma jam'iyyar ta amince da haka.
- Tabbatar da Umaru Damagum a matsayin shugaban jam'iyyar ta PDP har zuwa lokacin da za a gudanar da babban taron jam'iyyar a watan Nuwamba.
- Har wayau, Wike ya kuma bayar da sharaɗi cewa dole ne jam'iyyar ta amince da Chief Dan Orbih a matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na yankin kudu maso kudu wanda aka zaɓa a babban taron jam'iyyar na yankin da aka gudanar a Calabar da ke jihar Cross River.
- Barazana ta baya-bayan nan ita ce wadda Wiken ya yi ga babban taron jam'iyyar ta PDP da ta ce za ta a ranar 15 ga watan Nuwamban wannan shekarar a birnin Ibadan da ke jihar Oyo. Ana dai ganin adawar da Wiken ke yi wa taron da tsamin dantantakarsa da tsohon abokinsa, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.
- Ana ganin matsin lambar Wike ce ta tilasta wa jam'iyyar PDP kai talarar shugaban ƙasa a 2027 ga yankin kudancin Najeriya.
Me ya sa Wike ya gagari kowa a PDP?
To al'amarin da Wike abu ne da ya ƙi ci ya ƙi cinye sannan abu ne da ya ɗauki tsawon lokaci amma ba a iya yi masa komai ba duk da iƙrarin jam'iyyar na hukunta shi.
"Babban dalilin da ya sa ya gagari kowa shi ne yadda ya ɗauki dogon lokaci yana renon jam'iyyar bisa ƙudirinsa na yin takarar shugaban ƙasa a baya. Lokacin da ya ɗauka yana renon jam'iyyar ya sa wasu ƴan jam'iyyar na yanzu sun amfana da ayyukansa ta yadda a yanzu haka da wuya waɗanda suka ci moriyarsa su iya hukunta shi." In ji Malam Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano, CAS.
Masanin ya ƙara da cewa "wani dalilin da ya sa ba za a iya hukunta Wike ba a yanzu shi ne wasu manya da jiga-jigan jam'iyyar na ci gaba da ficewa daga PDP abin da ya sa ake ganin dole ne a ci gaba da yin haƙuri da shi kasancewar shi ne mai ƙarfi."
Illar rashin hukunta Wike
Malam Kabiru Sufi ya ce babbar illar da rashin hukunta masu laifi a jam'iyya ita ce "za a kai lokacin da wasu ƴan jam'iyyar su ma za su yi ƙarfi sannan za su iya ɗaukar irin matakin da Wike ke ɗauka kuma jam'iyyar ba ta isa ta yi komai tunda ba a kansu aka fara ba."
Yanzu Wike ya yi ƙarfi sosai sai dai kuma al'amura za su iya sauyawa inda wasu na daban su ma za su iya yin ƙarfin da ma ya fi nasa," in ji Malam Kabiru.
Ko Wike zai yi takara a 2027?
Ana iya cewa tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike, ya fi shahara a siyasar Najeriya ne tun bayan da ya saka zare tsakaninsa da shugabancin jam'iyyar PDP gabanin zaɓen 2023.
Tun daga lokacin ne yake kokawar neman iko da shugabannin jam'iyyar da ba su bin tafiyarsa, yayin da kuma yake ci gaba da riƙe muƙaminsa a gwamnatin Bola Tinubu ta jam'iyyar APC.
Babu tabbas ko har yanzu yana da sha'awar sake neman takara a PDP, amma idan bai haƙura ba to yanzu zai samu ƙwarin gwiwar shiga takarar kai-tsaye.
Sai dai kuma Wike ne mutumin da ake ganin ya yi wa jam'iyyar PDP matsin lamba wajen kai takarar shugaban ƙasa a 2027 ga yankin kudancin Najeriya.











