Gasar sarauniyar kyau da masu wasa a teku cikin hotunan Afirka

.

Asalin hoton, MOHAMED HOSSAM/EPA

Bayanan hoto, Mai niƙaya a Kogin Nilu
An wallafa

A ranar Asabar, wannan matashin ke ninƙaya a Kogin Nilu domin rage wa kansa raɗaɗin zafin rana da aka fuskanta a faɗin ƙasar Masar.

Rago

Asalin hoton, LEGNAN KOULA/EPA

Bayanan hoto, Rago ɗaure a Kasuwar Adibjan

Wani ƙaton rago kenan da aka ɗaure a kasuwar dabbobi ta birnin Abidjan, na ƙasar Ivory Coast, ranar Laraba gabanin bukukuwan Babbar Sallah.

.

Asalin hoton, YASUYOSHI CHIBA/AFP

Bayanan hoto, Masu rawa a Nairobi

Mambobin ƙungiyar maraya ta Kenya (DCK) ke gwaji a dandamali gabanin buɗe bikin rawa na "Cats" a birnin Nairobi ranar Juma'a.

.

Asalin hoton, LUIS TATO/AFP

Bayanan hoto, Masu wasan motsa jiki a Naiobi

Nan ma wata unguwa ce a Kenya, wasu masu wasannin motsa jiki ke gudanar da wani wasa a birnin Nairobi.

.

Asalin hoton, THOMAS MUKOYA/REUTERS

Bayanan hoto, Fursunoni a gidan gyaran hali na Nairobi

Gidan gyaran hali na mata kenan na Langata a birnin Nairobi, inda ake yi wa ɗaurarru mata kwalliya domin shiga gasar sarauniyar kayu tsakanin fursunoni ranar juma'a.

.

Asalin hoton, FEISAL OMAR/REUTERS

Bayanan hoto, Masu wasa tekun Indiya

Wani matashi ɗan Somaliya ya yi tsalle domin faɗa wa tekun Indiya a birnin Mogadishu ranar Juma'a.

..

Asalin hoton, TIKSA NEGERI/REUTERS

Bayanan hoto, Kona haramtattun makamai a Habasha

A ranar Laraba, jami'an 'yan sandan Habasha suka ƙona wasu bindigogi da suka kama a lokacin wani samame da suka ƙaddamar a wajen birnin Addis Ababa