Gasar sarauniyar kyau da masu wasa a teku cikin hotunan Afirka

An wallafa

A ranar Asabar, wannan matashin ke ninƙaya a Kogin Nilu domin rage wa kansa raɗaɗin zafin rana da aka fuskanta a faɗin ƙasar Masar.

Wani ƙaton rago kenan da aka ɗaure a kasuwar dabbobi ta birnin Abidjan, na ƙasar Ivory Coast, ranar Laraba gabanin bukukuwan Babbar Sallah.

Mambobin ƙungiyar maraya ta Kenya (DCK) ke gwaji a dandamali gabanin buɗe bikin rawa na "Cats" a birnin Nairobi ranar Juma'a.

Nan ma wata unguwa ce a Kenya, wasu masu wasannin motsa jiki ke gudanar da wani wasa a birnin Nairobi.

Gidan gyaran hali na mata kenan na Langata a birnin Nairobi, inda ake yi wa ɗaurarru mata kwalliya domin shiga gasar sarauniyar kayu tsakanin fursunoni ranar juma'a.

Wani matashi ɗan Somaliya ya yi tsalle domin faɗa wa tekun Indiya a birnin Mogadishu ranar Juma'a.

A ranar Laraba, jami'an 'yan sandan Habasha suka ƙona wasu bindigogi da suka kama a lokacin wani samame da suka ƙaddamar a wajen birnin Addis Ababa