Man United na son Jonathan, Crystal Palace na iya cefanar da Eberechi

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Arthur
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United ta bi sahun kungiyoyin Barcelona, da Bayern Munich da Real Madrid, a zawarcin mai tsaron gida na Jamus Jonathan Tah, mai shekara 29, idan kwantiraginsa ya kare da Bayer Leverkusen a kakar nan. (Sky Germany)

Crystal Palace ta shirya domin barin 'yan wasan Ingila Eberechi Eze, 26, da Marc Guehi, 24, su bar kungiyar a kakar nan. (Sun)

Chelsea ta zamo sahun gaba a zawarcin dan wasan tsakiya na Kamaru, Arthur Avom mai shekara 20. (Mirror)

Real Madrid na son Manchester United ta sake duba farashin fam miliyan 15 kan dan wasan Benfica, Alvaro Carreras, 22. Tun da fari kusan fam miliyan 27 ta so kan dan wasan bayan na Sifaniya daga Bernabeu, maimakon kashe fam miliyan 50 da kulub din na Prtugal ya bukata. (AS)

Arsenal na fatan dauko matashin dan wasan gaba na Palmeira, Luighi mai shekara 19, sai dai kungiyoyin Inter Milan da Borussia Dortmund na son dan wasan Brazil din. (Sun)

Bournemouth da Arsenal na daga cikin kulub din Premier League, da ke son mai tsaron ragar Sifaniya da ke taka leda a Espanyol Joan Garcia, 23. (Talksport)

Everton na son mai kai hari na Ipswich, Liam Delap, 22, sai dai ta na fuskantar barazana sakamakon kungiyoyin Chelsea da Manchester United. (Teamtalk)

Bournemouth na da kwarin gwiwar, za ta rattaba hannu kan sabon kwantiragi da manaja Andoni Iraola, inda zai bar kungiyar Tottenham. (Football Insider)

Kulub din MLS na Chicago Fire na tattaunawa da dan wasan tsakiya na Belgium, Kevin de Bruyne, 33, wanda ya ke shirin barin kungiyar Manchester City a karshen kakar wasa. (ESPN)

Como na tattaunawa da Manchester City, kan yiwuwar yarjejeniya ta dindindin, kan dan wsan tsakiya na Argentina ,Maximo Perrone mai shekara 22, wanda ya shafe kakar nan a zaman aro a kulub din Siri A. (Fabrizio Romano).

Leeds na duba yiwuwar dauko mai kai hari na Ingila da ke taka leda a Leicester, Jamie Vardy, 38, a daidai lokacin da suke shirin komawa Premier League da karfinsu. (Teamtalk)