Zaɓen Najeriya 2027: Ko PDP za ta kai labari ba tare da yin haɗaka ba?

Asalin hoton, @OfficialPDPNig
Matsayar gwamnonin PDP kan haɗakar jam'iyyun hamayya ya sa wasu ƴan Najeriya sun fara ɗiga ayar tambaya kan makomar jam'iyyar a zaɓen 2027.
A ranar Litinin ne gwamnonin PDP suka yi watsi da yunƙurin haɗaka da sauran jam'iyyun hamayya ba da nufin tunkarar zaɓen 2027.
Matsayar gwamnonin ta ci karo da iƙirarin tsohon ɗantakarar jam'iyyar kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar inda a kwanakin baya ya ce yana yunƙurin ƙulla haɗaka da wasu jam'iyyu.
Masana siyasa a Najeriya na ganin matsayar gwamnonin jam'iyyar PDP tana da ɗaure kai musamman yadda wasu ke ganin ba za ta iya kai labari ba idan ba ta haɗa kai da sauran jam'iyyun hamayya ba saboda rikicin cikin gida da ya dabaibaye ta.
Ana ganin akwai rarrabuwar kai tsakanin manyan jiga-jigan PDP musamman masu ruwa da tsaki ga tafiyar da harakokin jam'iyyar da kuma yadda za a saita alƙiblar jam'iyyar da makomarta kafin zaɓen 2027.
Haɗakar jam'iyyun hamayya ce ta kai ga haifar da jam'iyyar APC, kuma wannan ne ya ba sabuwar jam'iyyar ƙarfin doke PDP a zaben 2015.
Masharhanta dai na ganin sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a Najeriya ya nuna cewa idan da jam'iyyun hamayya sun dunƙule da sun karɓe mulki daga jam'iyya mai mulki ta APC.
Sai dai rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP wadda ake ganin ya kamata ta jagoranci haɗakar jam'iyyu a yanzu , babban ƙalubale ne ga jam'iyyar
Wasu na ganin sanarwar gwamnonin PDP alama ce da ke nuna akwai saɓani tsakaninsu da ɓangaren tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar.
PDP ba za ta kai labari ba - Atiku
Ɓangaren Atiku ya nace kan buƙatar cewa haɗakar jam'iyyu ce mafita domin samun nasarar zaɓen 2027.
"Atiku Abubakar yana kan bakarsa na ganin jam'iyyun hamayya sun haɗe domin fuskantar APC a zaben 2027," kamar yadda Abdulrasheed Shehu Sharaɗa mai taimaka wa tsohon mataimakin shugaban kasar kan harkokin yada labarai ya shaida wa BBC.
Amma Sharaɗa ya ce abin da gwamnonin PDP suka fito da shi ba zai zama abin da jam'iyyar PDP ta tsayu a kansa ba, inda ya ce Atiku zai tattaunawa da su domin fahimtar juna.
"Tattaunawar da muke yi da wasu jam'iyyu a yanzu ba mu kai ga batun jam'iyyar da za a mara wa baya ba, kuma ba muna nufin narkar da jam'iyyu ba, illa neman goyon bayan jam'iyyun hamayya kafin zaɓe," in ji shi.
Sharaɗa ya ƙara da cewa Atiku na ganin PDP ba za ta iya kai labari ba muddin ba ta yi haɗaka da wasu jam'iyyun hamayya ba
Matsayar shugabancin PDP
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugabancin PDP ya ce ya yi maraba da matakin da kungiyar gwamnonin jam'iyyar ta ɗauka tare da rufe ƙofar ɗunkulewa domin samar da wata sabuwar jam'iyya da niyyar tunkarar zaɓen 2027.
Jam'iyyar ta ce zaɓi ne na wani ɓangarenta da ke da'awar haɗaka da wasu jam'iyyu, musamman ɓangaren tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar da ya yi wa jam'iyyar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, kamar yadda Mataimakin Sakataren PDP na Ƙasa, Ibrahim Abdullahi ya shaida wa BBC.
Ya ce kasancewar PDP ita ce babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, "idan ma har hadaƙa ce cikinta ya kamata a yi takara."
A cewarsa ba zai yiyu ba a ce kana da gwamnoni 12, kana da ƴanmajalisa na dattawa kusan 40 da ƴan majalisar dokoki sama da 100 da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli kuma duk sai ka bar su a tafi wata jam'iyyar da wasu ke ganin ƙungiyoyi ne?
"PDP ta yarda a haɗa kai domin ƙwatar mulki daga hannun APC"
"Idan da gaske ake yi ai za a iya samun duk da nasarar da ake so idan an mara wa PDP baya, in ji mataimakin sakataren jam'iyyar PDP.
Ana zaman ƴanmarina a PDP
Masana na ganin idan har PDP tana son komawa kan mulki a Najeriya dole sai na nemi taimakon sauran jam'iyyun hamayya, la'akari da rikicin da ya dabaibaye ta.
Haka ma ƴan Najeriya da dama na zaton PDP za ta yi zawarcin ƴan'adawa domin a yi tafiya tare don tunkarar jam'iyyar APC a zaben 2027.
Farfesa Abubakar Kari na Jami'ar Abuja ya ce sanarwar gwamnonin PDP game da matsayarsu kan háɗaka tana da mamaki ganin irin ɗimbin rikicin da ya addabi jam'iyyar.
"Jam'iyyar na cike da rikici kuma a yanzu ƙarfinta ya ragu, yana da wahala ta iya cin zaɓe."
"Amma ba mu san ko gwamnonin suna da wani shiri ba ne na daban, domin yana da wahala wasu su shigo PDP ganin rikicin da take fama da shi" in ji Farfesa Kari.
Masanin ya ce irin wannan saɓani na zaman ƴanmarina a PDP da sauran jam'iyyun hamayya, na nuna jam'iyya mai mulki ce za ta fi cin gajiyarsa musamman na ganin jam'iyyun hamayya ba su háɗe ba.
Duk wata háɗaka da za a yi, PDP tana da damar ta yi mamaya saboda ƙarfin da take da shi na madafan iko a sassan Najeriya.
Masana na ganin zaɓin da ya rage wa PDP shi ne ta kashe wutar rikicin cikin gidanta musamman rarrabuwar kan yan jam'iyyar da kuma wasu ƴaƴan jam'iyyar da ke cikin gwamnatin jam'iyyar APC mai mulki.
Sannan masanan na ganin dole sai ta yi zawarcin wasu ƴan'adawa idan har tana son kai labari a zaɓen 2027.










