Waiwaye: Gwamnatin Buhari ta kai karar ASUU, ICPC ta bankado almundahanar ayyukan mazabu, da harin Batagarawa

An wallafa

Gwamnatin Buhari ta gurfanar da ASUU a gaban kotu

kungiyar ASUU

Asalin hoton, others

A ranar Litinin ne dai aka fara sauraron karar da gwamnatin Najeriya ta kai kungiyar malaman jami'o'i ta kasar ASUU a gaban kotun da'ar ma'aikata game da yajin aikin da suka kwashe wata bakwai suna yi.

A wata sanarwa da kakakin ma'aikatar kwadago ta kasar, Olajide Oshundun, ya fitar ya ce gwamnati ta dauki matakin ne bayan tattaunawa tsakaninta da kungiyar malaman jami'o'in ta ci tura.

Gwamnati tana son kotun da'ar ma'aikatan ta bai wa mambobin ASUU umarnin komawa bakin aiki, a yayin da ake ci gaba da shari'a a kan batun.

Haka kuma gwamnatin tana so kotu ta yi fashin-baki kan dokar kwadago mai sakin-layi 18 LFN 2004, musamman hukuncin yajin aiki a yayin da tattaunawa ke ci gaba tsakanin ministan kwadago da malaman jami'o'i.

Na yi namijin kokari a mulkina - Buhari

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Nagerian presidency

Sannan a makon da ya gabatan ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi namijin kokari, idan aka yi la'akari da dan abin da take samu wurin tafiyar da lamuran kasar.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin gudanar da ayyuka da dama duk da kudaden da take samu ba basa isa.

''Wannan gwamnati ta yi kokari sosai, dole na fada saboda wadanda alhakin fadar hakan ya rataya a wuyansu ba sa yin haka, ban san me ya sa ba,'' in ji Shugaba Buhari.

Shugaban ya yi kalaman ne yayin da yake jawabi a gidan gwamnatin jihar Imo da ke birnin Owerri ranar Talata, bayan bude wasu manyan ayyuka da Gwamna Hope Uzodinma ya yi.

ICPC ta bankado almundanar naira biliyan 2.8 na ayyukan mazabu cikin shekara uku

ICPC

Asalin hoton, Website/ICPC

A cikin makon da muke bankwana da shi din ne kuma hukumar da ke yaki da cin hanci da almundahanar kudade ta ICPC a Najeriya ta ce ta gano ayyukan mazabu da aka karkatar a fadin kasar da kudinsu ya kai naira biliyan 2.8

Hukumar ta ce ta gano hakan ne ta hanyar wani kwamiti da ta kafa don bin diddigin ayyukan mazabu a fadin kasar.

Wanda ya gano ayyukan mazabu kusan 2,444 da aka karkatar da kudinsu tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021 a fadin wasu jihohin kasar.

'Yan bindiga sun kai hari Batagawara a jihar Katsina in da suka sace mutane fiye da 50

'Yan bindiga

Mazauna kauyen Bakiyawa cikin yankin karamar hukumar Batagarawa a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, sun ce a ranar Larabar da ta gabata ne 'yan fashin daji suka kai musu hari, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da sace wasu fiye da 50.

Wani shaida daga garin na Bakiyawa, ya ce maharan sun je garin ne a kan Babura in da suka aiwatar da wannan aika-aika.

Ya ce maharan sun yi ta barin wuta a iska inda suka rika bi gida-gida suna daukar mutane.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa, ya tabbatar da kai wannan hari a kauyen na Bakiyawa da ke karamar hukumar Batagarawa, Inda yace sun yi arangama da ‘yan fashin dajin sosai.

PDP ta nada Tambuwal a matsayin daraktan yakin zaben Atiku

Tambuwal

Asalin hoton, PDP/Twitter

Haka kuma a ranar Alhamis ne babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar, inda ta nada gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal a matsayin babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasar

A wani sako da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce kwamitin wanda gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel ke shugabanta ya kunshi wasu gwamnonin da suka hada da gwamnan Ribas Nyesom Wike wanda ke ta kiraye-kirayen shugaban jam'iyyyar na kasa ya sauka daga mukaminsa.