An kai wa Salman Rushdie hari

Salman Rushdie

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An kai wa fitaccen marubucin nan Salman Rushdie, wanda aka kwashe shekaru da dama ana yi wa barazanar kisa bayan ya rubuta littafin The Satanic Verses, hari.

An kai masa harin ne yayin da yake jawabi a wurin wani taro a Jihar New York da ke Amurka.

Marubucin mai shekara 75, wanda ya lashe kyautar The Booker Prize, yana jawabi ne a Cibiyar Chautauqua yayin da aka kai masa hari.

Ganau sun ce sun ga wani mutum ya ruga a guje ya hau kan dandamalin da marubucin yake jawabi inda ya rika naushi yana kuma daba wa Mr Rushdie wuka a yayin da ake gabatar da shi gaban jama'a.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet ya nuna mahalarta taron sun ruga a guje kan dandamalin don kai masa dauki.

A halin yanzu ba a san halin da Mr Rushdie yake ciki ba.
Bayanan hoto, A halin yanzu ba a san halin da Mr Rushdie yake ciki ba.

Bayanai sun nuna cewa akwai alamun an daba masa wuka a wuya.

'Yan sandan Jihar New York sun ce mutumin ya hau kan dandamalin inda ya kai wa Mr Rushdie da mai yi masa tambayoyi hari.

"Alamu sun nuna cewa an ji wa Rushdie rauni da wuka a wuyansa," a cewar sanarwar da 'yan sandan suka fitar.

An garzaya da shi wani asibiti a cikin helikwafta, ko da yake babu cikakken bayani game da girman raunin da aka ji masa.

Rushdie

Marubucin dan asalin India ya shahara ne bayan ya rubuta littafi mai suna Midnight's Children a shekarar 1981, wanda aka sayar da kwafe fiye da miliyan a Birtaniya kadai.

Sai dai littafi na hudu da Mr Rushdie ya rubuta a 1988 - The Satanic Verses - ya tilasta masa shiga buya tsawon shekaru tara.

Littafin ya gamu da fushin Musulmai, wadanda ke ganinsa a matsayin batanci ga addini, inda aka haramta sayar da shi a wasu kasashe.

Shekara daya bayan wallafa littafin, Shugaban Addinin Iran Ayatollah Khomeini ya sanya ladan $3m (£2.5m) ga duk wanda ya kashe Mr Rushdie.

Mutane da dama ne suka mutu sakamakon tarzomar da ta barke kan wallafa littafin, ciki har da wasu da suka fassara littafin zuwa wasu harsunan.b