Juventus da Newcastle na son Phillips, Man City za ta karbo Oscar

Kalvin Phillips

Asalin hoton, OTHER

An wallafa

Juventus na tunanin siyan dan wasan Manchester City dan wasan tsakiyar Ingila Kalvin Phillips, mai shekaru 27. (Mail)

Ita ma Newscastle na duba yiwuwar siyan dan wasan a yayin musayar ‘yan wasan da za a yi a watan Janairu mai zuwa. (90 Min)

Shi kuwa kocin kungiyar Brentford Thomas Frank ya ce yana kyautata zaton dan gaban Ingila Ivan Toney mai shekara 27, zai ci gaba da kasancewa da kungiyar har sai bayan kakar musayar ‘yan wasan. (Standard)

Ikirarin na Frank wani koma baya ne ga Arsenal da Chelsea, wadanda ke sha’awar dan wasan Toney. (Mirror)

Newcastle na tunanin sake kiran dan wasan gaban Gambia Yankuba Minteh, mai shekara 19, daga aron da ya tafi Feyenoord domin ya taimaka mata cike gurbin ‘yan wasan da suka ji rauni. . (Telegraph - subscription required)

Su kuwa Manchester United da Newcastle na son daukar dan wasan Stuttgart dan kasar Guinea Serhou Giurassy mai shekara 27, a kan kudi fam miliyan 15. (Guardian)

Ange Postecoglou ya ce akwai yiwuwar Tottenham ta je kasuwar musayar ‘yan wasa domin siyan dan wasan tsakiya a watan Janairu mai zuwa yayin da yawancin ‘yan wasanta suka ji rauni ko kuma ba za su iya yin gogayya a gasar cin kofin Afirka ba. (Sky Sports)

Dan wasan Juventus dan kasar Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 23, ya fara tattaunawa da kungiyar a kan yiwuwar komawa Manchester United da Arsenal wadanda ke fatan daukarsa. (Gazzetta, in Italian - subscription required)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

West Ham na duba yiwuwar daukar dan wasan Crystal Palace dan kasar Faransa Odsonne Edouard a watan Janairu, yayin da dan tsakiyar Spaniya Pablo Fornals, mai shekara 27 kuma zai bar kungiyar. (Football Transfers)

Ita kuwa Liverpool na son kawo dan wasan Nice dan kasar Faransa Khephren Thuram zuwa Anfield. (Fichajes - in Spanish)

Tottenham da Brenford za su yi gogayya wajen siyan dan wasan PSV dan gaban Belgium Johan Bakayoko a watan Janairu mai zuwa. (Football Insider)

Raunin da dan wasan Manchester United dan kasar Netherland Tyrell Malacia na nufin wata dama ce ga dan bayan Spaniya Sergio Reguilon, mai shekaru 26, wanda ya ke matsayin aro daga Tottenham, ya ci gaba da zama a kungiyar. (Talksport)

Manchester City ta kusa kammala yarjejeniya a kan sabuwar kwantiragi da dan wasan Norway Oscar Bobb, mai shekara 20. (90 Min)

Barcelona ba zata biya fam miliyan 43 ba na kundin da aka sanyawa dan wasan gaba na Atletico Bilbao Nico Williams a sabuwar yarjejeniyarsa wadda zata ba wa dan wasan damar koma wa wata kungiya a bazara. (Mundo Deportivo - in Spanish)