Lyon ta kori kociyanta Grosso

Asalin hoton, Getty Images
Lyon ta kori kociyanta, Fabio Grosso, bayan wata bakwai yana horar da kungiyar.
Grosso, mai shekara 46 ya kai Lyon mai kofin gasar Faransa takwas matakin karshe a teburin bana, wanda ya ci wasa daya daga bakwai a lik.
An koreshi bayan mako 11 da ya maye gurbin Laurent Blanc a cikin watan Satumba.
Lyon, wadda rabonta da ligue 1 tun 2007-08 ta sanar da nada Pierre Sage a matakin wanda zai yi aikin rikon kwarya.
Ranar Lahadi Lille ta yi nasara a kan Lyon da ci 2-0, hakan ya sa kungiyaar ta ci gaba da zama da maki bakwai, bayan wasa 12.
Grosso, dan kasar Italiya tsohon dan wasan Lyon tsakanin 2007 zuwa 2009 ya ji rauni a wani harin da aka kai wa motar 'yan wasa a Marseille a cikin watan Oktoba.
Kociyan wanda ya ja ragamar Fronsinone zuwa Serie a bara, ya ci wasa daya a cikin watan Nuwamba a Ligue 1, shi ne wanda ya yi nasara a kan Rennes.
Tun farko sai a karshen kakar 2024 ya kamata kwantiraginsa ya kare a Lyon din.











