Abu biyar game da wasan Arsenal da PSG

Asalin hoton, PA Media
Kulob ɗin Arsenal zai karɓi baƙuncin ƙungiyar Paris Saint-Germain a filin wasa na Emirate a zangon farko na wasan kusa da ƙarshe a gasar nahiyar Turai da yammacin yau Talata.
Kulob ɗin ya kawo wannan matakin ne a gasar a karon farko tun shekarar 2009, lokacin da Manchester United ta lallasa ta.
Arsenal ɗin ta fitar da Real Madrid mai riƙe da kofi har karo na 15, a wasan dab da kusa da na ƙarshe.
Ita kuma ƙungiyar PSG ta yi waje da ƙungiyoyi biyu da ba ta ga maciji da su na gasar Premier, inda ta samu kai wa wasan dab da na ƙarshe a karo na huɗu tun 2019/20.
Ƙungiyoyin guda biyu dai sun fafata da juna a wannan kakar wasannin duk da cewa yaran Luis Enrique sun samu ci gaba tun bayan rashin nasarar da suka yi a wasansu a Emirate inda aka tashi 2-0 a watan Okotoba.
Ga wasu abubuwa guda biyar da ya kamata ku sani gabanin wasan ƙungiyoyin biyu:
Sun fafata sau shida a baya
Wannan ne dai zai kasance karon Arsenal da PSG na shida, kuma a wasanni biyar ɗin da suka gabata PSG ba ta samu nasara a kan Arsenal ba.
Arsenal ce ƙungiyar ƙwallon ƙafa da PSG ta fuskanta a gasar wasannin Turai kuma ba tare da samun nasara a kanta ba.
Shekaru 16 rabon da Arsenal ta kai wannan mataki
Arsenal za ta taka leda a wasan kusa da na ƙarshe na gasar zakarun turai a yau.
Lokaci na ƙarshe da ta samu irin wannan dama shi ne 5 ga watan Mayu na 2009 wato kwanaki 5838 ya zuwa yau.
Arsenal za ta yi fatan kafa tarihi a wannan lokaci, saɓanin a 2009 lokacin da Manchester United ta lallasa ta da ci 3-1 a gidanta.
Sun kara a zagayen farko
Arsenal ta casa Paris SG a watan Okotoba da ci 2-0 a Emirates a gasar ta Champions League.
Kulob ɗaya ne na Ingila da ya taɓa casa PSG sau biyu a zango ɗaya na gasa guda: Manchester City ta ci PSG a wasan kusa da na ƙarshe a 2020-21, (inda suka tashi wasa 2-1 a waje da kuma 2-0 a gida.)
PSG na shan wahala a Ingila
Paris SG ta gaza samun nasara a wasanninta guda biyar daga cikin shida da ta taka tsakaninta da ƙungiyoyin Ingila a gasar Champions League, inda ta yi rashin nasara a wasanninta biyu da Manchester City da kuma wasanta da Arsenal da Newcastle da Aston Villa.
Manyan 'yanwasa
- Ousmane Dembélé: Ya kasance yana da hannu kai tsaye wajen cin ƙwallaye 10 a kakar wasannin nan ta zakarun turai (season (ya ci ƙwallaye bakwai, ya taimaka an ci uku), kuma akwai yiwuwar goga kafaɗa da Kylian Mbappe na PSG wajen rawar da yake takawa a cin ƙwallaye, inda ya zura ƙwallaye takwas sannan ya taimaka aka ci uku, a 2020-21.
- Bukayo Saka: Shi kuma ya zura ƙwallaye guda tara sannan ya taimaka an ci ƙwallaye shida a wasanni 16 da ya taka wa Arsenal a gasar ta Champions League. Wannan ce taka rawar da ta fi kowacce ga wani ɗan wasan Ingila a kakar wasanni biyu a gasar, wadda kuma wani ɗan wasan gefe ya yi a wasanninsu guda biyu tun bayan tarihin da Sadio Mane ya kafa - wato 16 a kakar wasa ta 2017-18 da 2018-19.










