'Peter Obi ya zabi Datti Baba-Ahmed abokin takara ne ba don samun kuri'a ba'
'Peter Obi ya zabi Datti Baba-Ahmed a matsayin abokin takara ba, amma ba don samun kuri'a ba'

Masana harkokin siyasa a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan matakin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, ya dauka na zabar Dakta Datti Baba-Ahmed a matsayin mataimakinsa.
Masanan sun ce daukar Dakta Datti Baba-Ahmed, a matsayin abokin takara da Peter Obi ya yi, ba wani abu ba ne illa yana son ya nuna cewa yana da abokin takara ne daga Arewa.
Dakta Faruk Bibi Faruk, wanda malami ne a Jami’ar Abuja, ya shaida wa BBC cewa Peter Obi ya yi hakan ne ba wai don ya samu kuri’a ko goyon baya ba.
Ya ce “Dalilina na fadin haka kuwa shi ne Datti Baba-Ahmed, dan takara ne wanda a cikin shekarun da ya shafe yana siyasa ya samu ya je majalisar kasa sau daya.”
Malamin jami’ar ya ce mutum ne wanda yake siyasa mai akida, amma kuma marar jama’a.
Ya ce,” A maganganu da kuma irin alkibla ta siyasa a Najeriya, ya yi maganganu masu fa’ida a da, sannan ya dauki alkibla mai kyau a tafiyar siyasa, to amma ba shi da jama’ar da zai iya kawo wa dan takara dauki.”
Dakta Faruk Bibi Faruk, ya ce ana yi wa jam’iyyar Labour kallon ta ‘yan gurguzu, wato ta irin mutanen da ke kyamar masu arzikin da ba a san ta inda suka same shi ba, a yanzu ta zama jam’iyyar da take farautar duk inda mai danshi-danshi ya ke don ta ba shi dama yazo ya yi takara.
Ya ce, ‘’ Wannan ba abin da yakamata jam’iyyar mai rajin tafiyar da harkar kwadago ta kasa ta rinka yi ba ne, saboda Peter Obi cikakken dan kasuwa ne amma kuma ya samu takara a jam’iyyar.”
Malami Bibi Faruk ya kuma ce maimakon a ce an samu wani dan gurguzu ya goya masa baya, sai aka dauko wani hamshakin dan kasuwar aka jona tare.
Babban burin jami'yyar Labour, kamar sauran takwarorinta abokan hamayya shi ne ta kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC.
Sai dai wasu masana dai na ganin cewa jam'iyyar za ta fi tasiri ne a wani bangaren Najeriya, duk kuwa da daukar Datti Baba-Ahmed din a matsayin mataimaki.











