Coronavirus: Farashin Pogba ya fadi, Arsenal za ta sayar da Aubameyang

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Watakila Manchester United ta sayar da dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 27, cikin farashin da bai kai yadda ta sanya a baya ba sakamakon illar da annobar korona ta yi ga harkokin kudin kungiyoyin kwallon kafa. (Goal)

Arsenal za ta sayar da dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30, a kan £30m saboda ba ta so ya bar kungiyar a tsarin musaya ba tare da samun ko sisi ba. (Sun)

Har yanzu Arsenal bata ce za ta tsawaita kwangilar dan wasan Jamus Mesut Ozil, mai shekara 31 ba. (ESPN)

West Ham ba za ta sayar wa Chelsea dan wasan Ingila Declan Rice, mai shekara 21 ba. (Goal)

Newcastle da Everton sun bi sahun kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan Ajax da Netherlands Donny van de Beek. Manchester United da Real Madrid na cikin kungiyoyin da ke son dauko dan wasan mai shekara 23. (Le10 Sport - in French)

Everton ta sabunta kwantaragin dan wasan Real Madrid da Colombia James Rodriguez, mai shekara 28. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Arsenal da Manchester United suna sha'awar dauko dan wasan Monaco da Faransa Wissam Ben Yedder, mai shekara 29. (L'Equipe - in French)

Everton ta tattauna da Barcelona a kan dan wasan bayanta mai shekara 20, Jean-Clair Todibo. Yanzu haka dan wasan na Faransa yana zaman aro a Schalke. (Mail)

Liverpool ta soma tattaunawa da wakilin dan wasan Lille da Nigeria Victor Osimhen, mai shekara 21. (Le10 Sport - in French)

Newcastle na duba yiwuwar maye gurbin kocinta Steve Bruce da kocin Flamengo Jorge Jesus, wanda ya jagoranci tawagar Brazil wajen lashe Kofin Copa Libertadores na shekarar 2019(Goal)

Arsenal za ta biya Real Madrid euro 50m idan tana son sayen dan wasan Spaniya Dani Ceballos, mai shekara 23, wanda yake zaman aro a can. (AS - in Spanish)

Kazalika Arsenal tana fafutukar tsawaita kwangilar dan wasan Ingila mai shekara 18 Bukayo Saka a yayin da wasu kungiyoyin Premier suke ruguguwar dauko dan wasan. (90min)

Chelsea tana son dauko dan wasan Paris St-Germain mai shekara 17 Kays Ruiz-Atil, wanda kwangilarsa za ta kare a shekarar 2021. (L'Equipe - in French)