Coronavirus ta kashe sama da mutum 50

Asalin hoton, AFP
Hukumomin kasar China sun sanar da cewa sama da mutum 50 ne suka mutu sakmakon cutar Coronavirus, ya yin da wasu 2,000 suka kamu da cutar.
Yawancin wadanda suka mutu a birnin Wuhan ne, inda cutar ta fara bulla, ya yin da Henan da Shanghai nan ma cutar ke kara yaduwa.
Hukumoi a birnin Beijing da Shantou a gundumar Guangdong sun aike da sakon kar ta kwana na wayar salula, tare da umartar jama'a idan za su gaisa ba sai sun sha hannu ba.
Kidayar da hukumomi suka yi ta nuna kowanne mutum guda da ya kamu da cutar ya na shafawa akalla mutane 3.
Masana kimiyya na cibiyar hana cutuka yaduwa ta Birtaniya sun yaba wa Cana kan daukar lamarin da muhimmanci sun ce ya kamata arage yaduwarta da kashi 60 cikin 100.
Kuma babu alamun cewa China za ta iya shawo kan ci gaba da yaduwar wannan cuta.
Shugaba Xi Jingpin ya bayyana cewa hadarin da kasar ke ciki a dalilin wannan cuta ba karami ba ne, dan haka an haramta tarukan jama'a.
Tuni an takaita zirga zirga zuwa wasu birane musamman garuruwan da ke zagaye da birnin Wuhan inda cutar ta fara barkewa.
Haka ma za a gina asibiti na biyu a cikin mako uku, da za a kula da wadanda suka kamu da cutar 1,300 bayan wanda a ka kammala da ke daukar mutum 1,000.
Wata majiyar cikin gida na cewa an girke dubban likitoci da suka hada da na rundunar sojin kasar a yankin na Hubei da birnin Wuhan din ya ke.
Ko a shekarar 2003 Chana ta yi fama da cutar numfashi ta SARS, wadda ake samu daga dabbobi.
To sai dai wannan ne karon farko da a ka taba samun bullar wannan cuta da ke kama da SARS din.
Coronavirus na somawa ne da zazzabi da tari da kuma matsalar numfashi.
Kuma hukumomi sun zargi wata kasuwa dabbobi da ke gudanar da hada hadar dabbobin ba bisa ka'ida ba da alhakin bullar Coronavirus.









