Cutar Coronavirus na kara yaduwa a duniya

Corona Virus

Asalin hoton, AFP

An wallafa

Jami'an lafiya a China sun ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus ya karu.

Kawo yanzu mutane arba'in da daya ne suka mutu.

A China kawai, mutane sama da 1200 ne suka kamu da cutar.

Mace-mace na baya-bayan nan an same su ne a lardin Hubei inda cutar ta fara bulla.

Cutar Corona Virus

Asalin hoton, Getty Images

Kafar watsa labaran kasar ta ce wani likita wanda ya kula da marasa lafiyan a Wuhan ya mutu.

Asibitoci na fama da yawan marasa lafiya kuma wasu ba sa samun kula yadda ya kamata.

Kafofin yada labaran China sun ce an fara gina sabon asibiti mai gadaje 1000 don kula da marasa lafiya, kuma ana sa rai za a kammala ginin asibitin cikin kwanaki shidda.

Wuhan

A lokacin kuma da take kara bazuwa a China, haka ma a sauran sassan duniya.

An tabbatar da bazuwar ta a Turai inda mutum uku suka kamu da cutar a Faransa.

Ministar lafiya ta kasar, Agnes Buzyn ta ce daya daga cikin mutanen namiji ne wanda shekarunsa ba su haura hamsin ba, wanda kuma ya dawo daga birnin Wuhan a wannan makon.

Haka kuma, an samu cutar a Australiya da Amurka da Singapore da thailand da Vietnam.

Coronavirus

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana fuskantar karancin gadaje a asibitocin China saboda yadda cutar ta bazu