Lula da Silva: An sako tsohon shugaban Brazil daga kurkuku

Asalin hoton, AFP
An wallafa
Kotu ta saki tsohon shugaban Brazil Lula Da Silva bayn shafe shekara daya da rabi a gidan yari.
Dubban magoya baya ne suka yi masa maraba a harabar ofishin 'yan sanda a birnin Curitiba.
Mista Lula na kalubalantar hukuncin da aka yanke masa na daurin shekaru tara bisa zargin cin hanci.
To sai dai tsohon shugaban kasar ya ce wani bita da kullin siyasa ne da aka bullo da shi don hana shi takara a zaben da za'ayi badi.
Kawo yanzu shugaba Jair Bolsonaro bai ce komai ba game da sakin Mista Lula da Silva.







