Kamen Legas: Akwai jan aiki a gaban shugabannin Arewa

Matasan da gwamnatin Legas ta kama 'yan Jigawa

Asalin hoton, LAGOS STATE GOVERNMENT

Bayanan hoto, 'Yan sanda sun ce matasan da gwamnatin jihar Legas ta kama 'yan Jigawa su 121 ba masu laifi ba ne
An wallafa

Wani dan kasuwa kuma daya daga cikin shugabannin 'yan Arewa da ke zaune a jihar Legas ya yi gargadin cewa akwai jan aiki a gaban shugabannin Arewa, saboda katutun 'yan Arewar da ke tsare a jihar Legas.

Alhaji Ado Dansudu wanda ya shaida wa wakilin BBC haka bayan ceto wasu 'yan Arewar daga hannun hukumar jihar, ya ce akwai 'yan yankin arewacin Najeriyar da dama da ke tsare a kurkuku a jihar Legas wadanda aka kama ba tare da wani laifi da ya taka kara ya karya ba.

Jigon ya bayyana hakan ne kuwa bayan da suka yi kokarin ganin an sako matasan, wadanda rahotanni suka ce 'yan jihar Jigawa ne su sama da 120.

An dai tsare su ne bisa zargin kasancewarsu barazana ga jihar ta Legas.

Dan kasuwar ya ce sun shiga sun fita da taimakon sabon mai bai wa gwamnan jihar shawara Architect Ahmed Kabiru da kuma Kwamishinan 'yan sandan jihar Zubairu Mu'azu aka saki mutanen.

Alhaji Dansudu ya ce da yawa za ka ga an je da mota kawai an tsaya ana kama 'yan ci-rani 'yan Arewa wasu da dama ba sa jin Turanci ba sa jin Yarabanci, sai a kai su kotu kawai a yi masu hukuncin dauri.

'Yan sandan Najeriya na sintiri

Asalin hoton, Getty Images

Ya kara da cewa kuma ko da cewa aka yi dan Arewar ya kashe mutum saboda ba ya jin yaren garin cewa zai yi eh, in ji Dansudu.

Ya ce akwai da yawa 'yan Arewa wadanda suke tsare a gidan yari wadanda ba su ji ba ba su gani ba, amma an daure su.

Shugaban kungiyar dattawan arewacin Najeriya, Northern Elders Forum, Farfesa Ango Abdullahi
Bayanan hoto, Shugaban kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya, Northern Elders Forum, Farfesa Ango Abdullahi

Shugaban ya ce ya kamata manyan Arewa su je Legas su je gidajen yari domin ceto irin wadannan 'yan yankin da aka kama aka tsare ba tare da wani laifi ba, ko kuma laifin da ba wani babba ba ne.

Gwamnatin jihar Legas takan kama mutane masu kananan sana'o'i a titunan jihar bisa zargin cewa suna bata muhalli da sa kazanta tare da haifar da cunkoso a yankunan da ba su dace ba.