Karim Benzema ne gwarzon Champions League na bana

Asalin hoton, Getty Images
An bayyana dan wasan Real Madrid, Karim Benzema a matakin gwarzon Champions League na kakar 2021/22.
Dan kwallon tawagar Faransa, mai shekara 34, ya lashe kofin Zakarun Turai na biyar kenan, bayan da Real ta doke Liverpool 1-0 ranar Asabar a Faransa.
Ya kuma ci kwallo 15 a karawa 12 a Champions League a bana, wanda ke kan gaba a takarar kyautar Ballon d'Or ta kakar nan.
Shi kuwa Vinicius Jr. wanda ya ci Liverpool kwallon, an bayyana shi a matakin matashin da ba kamarsa a babbar gasar Zakarun Turai ta bana.
Mai sekara 21 ya ci kwallo hudu ya kuma bayar da shida aka zura a raga a kakar ta 2021/22.
'Yan wasa biyu suna daga cikin 11 da suka fi bajinta a Champions League har da Luka Modric da mai tsaron raga, Thibaut Courtois, wanda shi ne yafi taka rawar gani a ranar Asabar.
Liverpool wadda ta yi rashin nasara tana da 'yan kwallo hudu daga 11 fitattu a gasar bana da suka hada da Trent Alexander-Arnold da Virgil van Dijk da Andy Robertson da kuma Fabinho.
Sauran 'yan wasa 11 da ba kamarsu a Champions League a kakar nan sun hada da dan kwallon Paris St-Germain, Kylian Mbappe da na Manchester City, Kevin de Bruyne da kuma Antonio Rudiger na Chelsea.









