Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Raphinha, Lewandowski, Origi, Rudiger, Mitchell

Raphinha

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Leeds ta sayo Raphinha ne daga Rennes a 2020 kan kudin da ake gani ya kai fam miliyan 17 da sauran tsarabe-tsarabe tsawon shekara hudu
An wallafa

Barcelona ta bi sahun Liverpool da Manchester City da kuma Bayern Munich a fafutukar zawarcin dan gaba na gefe na Leeds kuma dan Brazil Raphinha, mai shekara 25, wanda kungiyarsa ta yi masa farashi fam miliyan 60. (Mirror)

Haka kuma Barcelona na sha'awar Robert Lewandowski, na Real Madrid kuma kyaftin din tawagar Poland mai shekara 33. (Sport - in Spanish)

Robert Lewandowski,

Asalin hoton, Reuters

Dan gaban Liverpool Divock Origi, mai shekara 26, na tattaunawa da abokan hamayya na gasar Italiya ta Serie A, AC Milan da Inter Milan a kan komawarsa daya daga cikinsu idan kwantiraginsa ya kare da Liverpool a bazara. (90min)

Manchester City na daga cikin kungiyoyin Premier da ke sa ido a kan dan wasan baya na gefe na Crystal Palace, Tyrick Mitchell bayan da dan bayan mai shekara 22 ya samu goron gayyata zuwa tawagar Ingila a karon farko.(Sun)

Dan bayan Chelsea Marcos Alonso, mai shekara 31, ya ce zai so ya sake taka leda a gasar La Liga idan ya samu dama. Dan Sifaniyar ya yi wa Real Madrid wasa daya ne kawai na gasar lig tun da ya taso daga tawagar renon matasan 'yan kwallon kungiyar. (AS - in Spanish)

Hankalin kyaftin din Chelsea Cesar Azpilicueta, mai shekara 32, ya rabu biyu tsakanin sanya hannu a sabuwar yarjejeniya ta karin shekara daya a kungiyar ko kuma ya yarda ya tafi Barcelona a kwantiragin shekara daya. (Express)

Cesar Azpilicueta

Asalin hoton, Getty Images

Dan bayan tawagar Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 29, ka iya kasancewa dan bayan Chelsea na uku da zai bar Stamford Bridge saboda kwantiraginsa zai kare a bazara, kuma Juventus ta gabatar masa da tayi. (Sky Sports)

Arsenal da Tottenham na bukatar biyan fam miliyan 20, idan har wata daga cikinsu na son sayen dan bayan Middlesbrough Djed Spence, mai shekara 21, wanda tauraruwarsa ke haskawa a zaman aron da yake yi a Nottingham Forest. (Express)

Benfica da Sporting Lisbon na sa ido a kan dan wasan Barcelona Francisco Trincao, ko da dan wasan mai shekara 22 da ke zaman aro a Wolves ba zai ci gaba da zama na dindindin ba a kungiyar a kan fam miliyan 25. (Record - in Portuguese)

Shi kuwa gwanin matashin dan wasan tsakiya na Barcelona, dan Sifaniya Gavi, mai shekara 17, da dan bayan Uruguay Ronald Araujo sun yi watsi da tayin da Barcelona ta yi musu na sabon kwantiragi. (Marca - in Spanish)

Dan gaban Blackburn da tawagar kasar Chile Ben Brereton Diaz, mai shekara 22, na daukar hankalin kungiyar Sevilla, inda kungiyar ta La Liga ke son sayensa domin zama lamba taranta. (Estadio Deportivo - in Spanish)

Watakila West Ham ta kara taya dan gaban Benfica dan Uruguay Darwin Nunez, bayan da kungiyar tasa ta yi watsi da tayin fam miliyan 50, da ba a taba yi wa wani dan wasanta ba a tarihi a kan dan wasan mai shekara 22 a watan Janairu. (Standard)

Leeds na sha'awar sayen Ryan Kent dan Ingila daga Rangers, inda dan wasan mai shekara 25 yake da sharadin kudin na-gani-ina-so fam miliyan 20 a kwantiraginsa.(Football Insider)