Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Nkunku, Bastoni, Abraham, Morata, Gnabry

Christopher Nkunku

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Christopher Nkunku
An wallafa

Chelsea na duba yiwuwar saye dan wasan RB Leipzig da Faransa mai buga gaba Christopher Nkunku, dan shekara 24.(Goal)

Kungiyar na kuma iya jan kafa wajen dauke dan wasan Monaco da Faransa da ke buga tsakiya, Aurelien Tchouameni, mai shekara 22, ita ma dai Real Madrid na harin dan wasan. (Goal)

Tottenham na sa ido kan dan wasan Inter Milan Alessandro Bastoni, mai shekara 23, hakazalika ita ma Manchester United. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

An duba lafiyar mai tsaron raga a Ingila Fraser Forster a kokarin komawa Tottenham idan kwantiraginsa ya kare da Southampton a wata mai zuwa. (Mail)

Arsenal na nuna zawarci kan Alvaro Morata. Dan wasan Sifaniya mai shekara 29, ya shafe wannan kaka yana zaman aro a Juventus daga Atletico Madrid. (Tuttosport - in Italian)

Gunners na harin Tammy Abraham yayinda dan wasan ke cewa yana jindadin zaman sa a Roma, sai dai kuma yaki nuna matsayarsa kan yiwuwar komawa kungiyar ta Firimiya a sabuwar kaka. (Metro)

Arsenal ta kuma nuna zawarcinta kan dan wasan Jamus Serge Gnabry daga Bayern Munich sai dai ba lallai ta iya sayensa ba a wannan kaka. (Christian Falk)

Arsenal ta gabatar da tayin karshe kan dan wasan Ingilar nan mai shekara 22 Eddie Nketiah - kuma akwai yiwuwar ya sanya hannu domin ci gaba da zama da kungiyar a wannan kaka. (Mail)

Aston Villa a shirye take ta soma farautar dan wasan nan mai shekara 22 da ke taka leda a Rangers dan asalin Najerita Calvin Bassey. (Times)

Barcelona ta tattauna da wakilan dan wasan Villa da Ingila Carney Chukwuemeka, mai shekara 18. (Sport - in Spanish)

Paris St-Germain na iya sayer da dan wasan Brazil da ke buga gaba Neymar, mai shekara 30, idan ta samu tayi mai gwabi. (Goal)

Liverpool ta sa dan wasanta a kasuwa Alex Oxlade-Chamberlain, mai shekara 28, yayinda Aston Villa da West Ham suka nuna zawarcinsu (Mirror)

Tattaunawa tsakanin dan wasan West Ham da Czech, Tomas Soucek, kan sabuwar yarjejeniya ta kai wani mataki. (Guardian)

Everton da Crystal Palace na farautar dan wasan Brazil Ederson Silva, mai shekara 22, da ke taka leda a kungiyar Seria A ta Salernitana. (Football Insider)

Dan wasan Everton mai shekara 25 Jonjoe Kenny, wanda a yanzu kwantiraginsa ya kare, ya soma nuna alamomi kan makomarsa a gaba.(Liverpool Echo)

Mai bugawa Jamus tsakiya Pascal Gross, dan shekara 30, na tattaunawa da Brighton kan sabuwar yarjejeniya. . (Kicker - in German)