An yi bikin bai wa Bayern Munich Bundesliga na bana

Robert Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An bai wa Bayern Munich, Bundesliga na bana da ta lashe, bayan 2-2 da Stuttgard a wasan mako na 33 a babbar gasar tamaula ta Jamus.

A karawar ta ranar Lahadi, Konstantinos Mavropanos ne fara cin gida, sannan Thomas Mueller ya ci wa Bayern kwallo na biyu.

Stuttgard ta ci kwallayen ta hannun Tiago Tomas da kuma Sasa Kalajdzic.

Bayan da saura wasa daya ya rage a kammala gasar bana, Bayern ta ci wasa 24 da canjaras hudu aka doke ta biyar.

Kungiyar mai maki 76 ta ci kwallo 95 aka zura mata 35 kawo yanzu.

Bayern Munich ta lashe Bundesliga na 10 a jere kuma na 32 jumulla.

Borussia Dortmund ce ta biyu wadda ta yi nasara a karawa 21 da canjaras uku aka doke ta wasa tara ta ci kwallo 83 aka zura mata 51 ta hada maki 66.

Wadanda suke kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga:

  • Robert Lewandowski FC Bayern Munich 34
  • Patrik Schick Bayer 04 Leverkusen 24
  • Erling Haaland Borussia Dortmund 21
  • Christopher Nkunku RB Leipzig 20