Wasan Liverpool da na Real Madrid da suka rage kafin su kara a Champions League

Ancelotti and Klopp

Asalin hoton, Getty Images and Reax

An wallafa

Real Madrid da Liverpool za su fafata a wasan karshe a Champions League na bana ranar 28 ga watan Mayu a Faransa.

Liverpool ta kawo wannan matakin bayan da ta fitar da Villareal, ita kuwa Real Madrid nasara ta yi a kan Manchester City.

Tuni Real Madrid ta lashe kofin La Liga na bana, bayan da Liverpool ke harin cin kofi biyu kafin su fafata a wasan karshe a Gasar Zakarun Turai ta bana.

Sauran wasa hudu ya rage da Real Madrid za ta buga a La Liga, wadda za ta fuskanci karawar hamayya da Atletico Madrid a Wanda Metropolitano ranar Lahadi.

Daga nan za ta karbi bakuncin Leavante ranar Alhamis, sannan ta ziyarci Cadiz kwana uku tsakani, sai ta karkare da wasa da Real Betis a Santiago Bernabeu.

Wasannin za su yi tsauri a karawa da Atletico Madrid da Real Betis, wadanda ke neman gurbin shiga Champions League a badi.

Haka kuma Real za ta fuskanci kalubale a karawar da za ta yi da Levante da kuma Cadiz, wadanda ke fuskantar barin babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana.

Sai dai Real Madrid za ta so ta ci gaba da zama kan ganiya kafin wasan karshen, hakan ne zai sa ta ajiye wasu 'yan wasan su huta kafin karawar karshe a Champions League, damar da Liverpool ba ta da ita kenan.

Liverpool tana ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester City mai jan ragama, kuma mai rike da kofin bara.

Liverpool za ta karbi bakuncin Tottenham a Anfield ranar Asabar, daga nan ta ziyarci Aston Villa ranar Talata.

Daga nan Liverpool za ta kece raini da Southampton a St Mary ranar 17 ga watan Mayu, sannan ta karkare kakar bana a Premier da karawa da Wolverhampton Wanderers ranar 22 ga watan Mayu.

Liverpool za ta buga wasan karshe a FA Cup ranar 14 ga watan Mayu da Chelsea, wadda za ta dauki fansa, bayan da kungiyar Anfield ta yi nasarar cin Caraboa Cup a bana.

Liverpool wadda ta lashe Caraboa Cup na fatan cin kofi hudu a bana, ba wata kungiya a Ingila da take da wannan bajintar.

Liverpool na sa ran daukar FA da Premier League da kuma Champions League ta hada da Caraboa Cup da ta fara ci a bana.

Real Madrid tana da Champions League 13 jumulla, ita kuwa Liverpool shida ne da ita.