Kasuwar 'yan wasa: Mbappe, Ziyech, Werner, Pochettino, Conte da sauransu

Asalin hoton, Getty Images
A karshen kakar nan kwantiragin Kylian Mbappe zai kare a Paris St Germain, ana cewa Newcasle United tana daga cikin kungiyoyin da za su nemi daukarsa a badi. (Express)
Ana hangen watakila dan wasan Chelsea, Hakim Ziyech da Timo Werner daya daga ciki zai maye gurbin Raheem Sterling, wanda ake cewar zai koma Barcelona a watan Janairu. (ESPN)
An yi watsi da tayin da Manchester United have ta yi wa kociyan Paris St-Germain, Mauricio Pochettino. (Manchester Evening News)
Tsohon wanda ya horar da Tottenham da kuma Southampton, Pochettino, mai shekara 49, zai ci gaba da jan ragamar PSG nan da wata shida, sannan ya karbi jan ragamar United. (Star)

Asalin hoton, Getty Images
Sabon kociyan Tottenham, Antonio Conte ya tattauna da mahukuntan kungiyar kan batun a sayo masa dan wasan Manchester United, Eric Bailly, mai shekara 27. (Transfer Window podcast, via Express)
Manchester United ta tattauna da tsohon kocin Borussia Dortmund da Lucien Favre da wanda ta taba kocin Lyon, Rudi Garcia domin bai wa aikin jan ragamar Manchester United. (Telegraph)
Haka shima Ralf Rangnick wanda ya horar da RB Leipzig da tsohon kocin Roma, Paulo Fonseca suna daga cikin jerin masu horar da tamaula da United za ta tuntuba. (Mail)
Liverpool da Barcelona na son daukar dan wasan Chelsea, Christian Pulisic, mai shekara 23, sai dai Blues ba za ta sayar da shi ga abokiyar hamayya ba, sannan kungiyar Barcelona ba ta da kudin da za ta sayi dan wasan kan Yuro miliyan 50. (El Nacional, in Catalan)

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta tattauna kan batun daukar dan kwallon Fenerbahce mai tsaron baya, Attila Szalai, 23. (Football Insider)
Kungiyoyi da dama na bibiyar dan wasan Arsenal, Alexandre Lacazette kan kwantiraginsa da zai kare a karshen kakar bana, ciki har da Atletico Madrid da Barcelona da Newcastle da kuma AC Milan. (Calciomercato)
Gunners na fatan daukar dan kwallon Lille, Renato Sanches, mai shekara 24, a watan Janairu idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai. (Football London)

Asalin hoton, Sky soprt
Dan wasan Manchester United, Jesse Lingard, mai shekara 28, har yanzu na fatan barin Old Trafford duk da cewar an kori Ole Gunnar Solskjaer's exit. (Star)
Mason Mount, mai shekara 22, bai damu da makomarsa a Chelsea ba, duk da yanayin da yake ciki kan yarjejeniyarsa - ya ce yana fatan lashe kofuna a kungiyar ta Stamford Bridge. (Telegraph)
Newcastle United za ta yi gogayya da Manchester United wajen daukar dan kwallon Atletico Madrid, Kieran Trippier, mai shekara 31. (Sun)
Watakila sabon kocin Newcastle, Eddie Howe, mai shekara 43, ya fara jan ragamar kungiyar a ranar Asabar a gasar Premier League da Arsenal duk da kamuwa da ya yi da cutar korona. (Mail)









