Kasuwar 'yan wasa: Werner, Pogba, Camavinga, Partey, Ozil, Neymar

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta shaida wa wakilan Timo Werner cewa tana bukatar karin lokaci domin yanke shawara kan ko hukumance za su taya dan wasan na RB Leipzig mai shekara 24, a yayin da suke jira don ganin irin tasirin da annobar korona ta yi a kan kasuwar musayar 'yan kwallon kafa, a cewar jaridar Guardian.
Inter Milan tana shirin yin musaya wacce a bangare guda za ta hada da bai wa Leipzig dan wasan Austria Valentino Lazaro, mai shekara 24, wanda yake zaman aro a Newcastle. (Tuttosport - in Italian)
Real Madrid na shirin dauko dan wasan tsakiyar Faransa da ke buga wasa a Manchester United Paul Pogba, mai shekara 27. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Kazalika Real tana son dauko matashin dan wasan Rennes Eduardo Camavinga, a yayin da ita ma Old Trafford take zawarcin dan wasan mai shekara 17. (AS - in Spanish)
Haka kuma Madrid tana son dauko dan wasan Sao Paulo Igor Gomez ko da yake har yanzu bata bayyana bukatar dauko dan wasan mai shekara 21 ba a hukumance. Barcelona, Sevilla da Ajax suna son sayo dan wasan na Brazil. (Goal via Globo Esporte)
Dan wasan tsakiya na Atletico Madrid Thomas Partey, mai shekara 26, ya fito ya bayyana cewa yana son komawa Arsenal inda yake fatan kungiyoyin biyu za su kulla yarjejeniya yadda shi kuma Alexandre Lacazette zai koma Madrid. (Telegraph)
Tsohon dan wasan Aston Villa Nii Odartey Lamptey ya gargadi Partey a kan komawa Ingila. Kungiyoyin Juventus da Inter Milan suna son dauko dan wasan na Ghana. (Standard)
Rahotanni sun ce kungiyar Fenerbahce da ke Turkiyya tana yunkurin dauko dan wasan Arsenal Mesut Ozil, mai shekara 31 kafin kwangilarsa ta kare a shekara mai zuwa. (Sun)
Har yanzu dan wasan Brazil Neymar yana son barin PSG domin sake komawa Barcelona inda aka yi amannar cewa dan wasan mai shekara 28 zai amince a rage 50% na albashinsa don kawai ya koma Spaniya. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Newcastle za ta biya Tottenham £12.5m idan tana son nada Mauricio Pochettino a matsayin kocinta a wannan watan - ko da yake za su iya dauko shi ba tare da bayar da ko sisi ba bayan ranar 31 ga watan Mayu. (ESPN)
Tsohon kocin Bayern Munich Jupp Heynckes ya yi amannar cewa ana zuzuta dan wasan Manchester City dan kasar Jamus Leroy Sane, mai shekara 24, wanda ake rade radin cewa zai koma Munich, inda ya ce bai kama a 'kashe har £100m don sayo dan wasan'. (Independent via Sport Bild)
Arsenal da Chelsea za su fafata domin dauko dan wasan Feyenoord Orkun Kokcu, mai shekara 19, wanda za a sayar a kan £23m. (Sun)
Leicester City za ta dauko dan wasan Jamus Ismail Jakobs amma FC Koln tana son a biya ta £9m. (Leicester Mercury via Todo Fichajes)









