Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Rice, Mbappe, Danjuma, Guardiola, Lampard, Nunez

An wallafa

Manchester United na shirin daukar mataki irin sa na farko game da sayen 'yan wasan inda suke son dauko dan wasan West Ham da Ingila Declan Rice, mai shekara 23. (90 Min)

Kazalika Manchester United na aiki tukuru wajen ganin ta dauki dan wasanLeeds United da Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 26. (Manchester Evening News)

Old Trafford ta shaida wa 'yan wasa sida cewa za su iya yin gaba a bazarar nan. (Mirror)

Paris St-Germain ta yi wa dan wasan Faransamai shekara 23 Kylian Mbappe, wanda kwantaraginsa zai kare a bazara, tayin makudan kudin da suka kai yuro 150m (£125m) domin ya ci gaba da zama tsawon kaka biyu. (Guillem Balague)

Kylian Mbappé

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta tura jami'anta domin kallon wasan dan kwallon Villarreal Arnaut Danjuma a fafatawar da za su yi da Bayern Munich ranar Laraba, a yayin da Liverpool ma ke son daukar dan wasa mai shekara 25 dan kasar Netherlands. (Mail)

Pep Guardiola

Asalin hoton, Reuters

Brazil na shirin bai wa kocin Manchester City Pep Guardiola makudan kudi domin ya zama kocin kungiyar kwallon kafar kasar. (Marca)

Kocin Everton Frank Lampard ya samu goyon bayan mai kungiyar kwallon kafar Farhad Moshiri da kuma majalisar zartarwar Goodison Park, duk da cewa ana dab da fiatr da Toffees daga Gasar Firimiya. (Mail)

Newcastle da West Ham na son daukar dan wasan Union Berlin da Najeriya Taiwo Awoniyi, mai shekara 24, a bazarar nan. (Sun)

An shaida wa Arsenal, Manchester United da Tottenham cewa sai sun biya £67m idan suna son daukar dan wasan Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 22, daga Benfica. (Express)

Arsenal na son daukar dan wasan Aston Villa da Ingila Ezri Konsa, mai shekara 24. (Football Insider)