Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Neves, Pogba, Danjuma, Werner, Depay, Gakpo, Lukaku

An wallafa

Idan aka nada kocin Ajax Erik ten Hag matsayin sabon kocin Manchester United kamar yadda ake tsammani, zai nemi daukar dan wasan tsakiyar Portugal Ruben Neves, mai shekara 25, daga Wolves. (Sun)

Kazalika Ten Hag dan kasar Netherlands yana son daukar dan wasan Ajax da Netherlands Jurrien Timber domin su tafi Old Trafford. (Star)

Dan wasanManchester United Paul Pogba, mai shekara 29, ya fi son komawa Juventus maimakon Paris St-Germain idan kwantaraginsa ya kare a bazara, sai dai kungiyar ta kasar Italiya tana shakku kan dawo da shi saboda bukatunsa na albashi da alawus-alawus da kuma ganin ya soma tsufa. (Tuttosport - in Italian)

Sadio Mane

Asalin hoton, GEOFF CADDICK

Bayanan hoto, Sadio Mane

Liverpool na kallon dan wasan Villarreal dan kasar Netherlands Arnaut Danjuma, mai shekara 25, a matsayin wanda zai iya maye gurbin dan wasanta dan kasar Senegal mai shekara 29 Sadio Mane, sai dai ana sa rai kungiyar ta Reds ba za ta nemi daukarsa ba sai 2023. (Goal)

Brighton ba ta da niyyar sayar da golanta Robert Sanchez a yayin da Newcastle take zawarcin dan kasar Sifaniya mai shekara 24. (Football Insider)

Wakilin dan wasan Chelsea da Jamus Timo Werner, mai shekara 26, ya tafi Italiya inda yake ganawa da shugabannin AC Milan, Juventus da Atalanta. (Corriere dello Sport - in Italian)

Arsenal, Everton da Newcastle duka sun nuna sha'awar daukar dan wasan Netherlands mai shekara 28 Memphis Depay daga Barcelona. (Superdeporte - in Spanish)

Romelu Lukaku

Asalin hoton, PA Media

Dan wasanPSV Eindhoven da Netherlands Cody Gakpo, mai shekara 22, ya bayyana irin kaunar da yake yi wa Arsenal a yayin da ake ci gaba da alakanta shi da wasu kungiyoyin Gasar Firimiya da suka hada daManchester United da Liverpool. (Goal)

Manyan jami'ai a Inter Milan yanzu suna son dan wasan Chelsea da Belgium Romelu Lukaku ya koma kungiyar tasu. (Mirror)

Leicester City na sha'awar daukar dan wasan FC Mainz dan kasar Netherlands Jeremiah St. Juste, mai shekara 25. (Bild - via Leicester Mercury)