Dalilai hudu da watakila Frankfurt ta doke Barcelona

Eintracht Frankfurt

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Barcelona ta ziyarci Eintracht Frankfurt, domin buga wasan zangon farko a Europa League da za su kece raini ranar Alhamis a Jamus.

Barcelona ta fafata da kungiyoyin Jamus 18, amma wannan shine karon farko da za ta fuskanci Frankfurt a gasar Zakarun Turai, in banda haduwa da suka yi a wasan sada zumunta a 1970.

Barcelona tana mataki na biyu a teburin La Liga, wadda ta yi wasa 13 ba tare da an doke ta ba a dukkan fafatawa, rabon da ta ta yi rashin nasara tun a Copa del Rey 3-2 a hannun Bilbao a cikin watan Janairu.

Ita kuwa kungiyar Jamus wadda itace ta rage da ta lashe kofin, tana ta tara a gasar Bundesliga ta bana, bayan da ta yi nasara a karawa uku daga takwas da ta yi a 2022.

A hasashe ana ganin Barcelona ce za ta yi nasara a kan kungiyar Jamus, sai ddai kuma da akwai wwasu dalilai da Frankfurk ka iya cin kungiyar Camp Nou.

1. Kungiyar Jamus kan samu nasara a kan na Sifaniya

Frankfurt ba ta taba yin rashin nasara a hannun kungiyoyi daga Sifaniya a Europa ba, in banda a karawar karshe.

A wasa bakwai da Frankfurt ta yi a Europa League, UEFA Cup da kuma UEFA Cup Winners da kungiyar La Liga, ba ta taba yin rashin nasara ba.

Wasan da ta yi rashin nasara shine a Champions League a Mayun 1960 da ci 7-3 a hannun Real Madrid.

2. Frankfurt tana buga salon wasa iri daya da na Barcelona

Magoya bayan Frankfurt sama da dubu 250 ne suka bukaci sayen tikitin kallon karawa da Barcelona, kenan filin da ke cin 'yan kallo 48,500 zai cika makil kenan.

Koci, Oliver Glasner ya kwwan da sanin salon Barcelona karkashin Xavi Hernandez, za su yi iya kokari su mamaye karawar da kuma rike kwallo a koda yaushe.

Kungiyar Jamus ta iya salon taka leda iri daya da na Barcelona, kum tafi yin sa a waje, wadda itace ta hudu a samun sakamakon mai kyau a Bundesliga a waje, wadda ta hada maki 22 daga 39 da yake kasa a karawar waje.

3. Filip Kostic ya yi suna wajen bayar da kwallo a zura a raga

Dan kasar Serbia ya koma Eintracht a 2018, wanda ake cewa zai kawo karshen zamansa a kungiyar a karshen bana, wasu magoya bayan kungiyar suna fatan ya tsawaita zamansa.

'Yan wasa biyar ne, wadanda ba sa cikin 'yan hudun farko a Bundersliga suka bayar da kwallaye aka zura a raga, fiye da Kostic mai takwas a karawa 25 da ya yi a kakar nan.

4. Sun kware a cin kwallo a mintin karshe

Frankfurt da Lyon da Monaco da kuma Galatasaray sune suka kawo wannan matakin ba tare da doke su ba a gasar bana, haka kuma kungiyar Jamus ta yi fice a cin kwallo a mintin karshe.

Dan wasanta, Goncalo Paciencia ya ci Antwerp 1-0 a bugun karshe a karin lokoci a waje, a wasan farko a cikin rukuni, haka kuma dan kasar Portugal ya kara a wasa na biyu.