Mohamed Salah: Ban tsauwala ba a sharudan sabunta yarjejeniyata da Liverpool

Mohamed Salah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohamed Salah
An wallafa

Dan wasan gaban Liverpool Mohamed Salah ya ce buƙatun da yake neman kungiyar ta biya shi a sabuwar kwangilar da take so ya sanya wa hannu ba wasu ''masu tsauri'' ba ne.

Dan wasan dan kasar Masar, wanda a watan Yuni zai cika shekara 30 a duniya kuma saura wata 18 kwangilarsa ta kare, ya ce ya rage wa kungiyar ta nuna godiya kan nasarorin da ya taimaka mata ta samu.

A baya Salah ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da zama a kungiyar.

"Ina son ci gaba da zama [a kungiyar nan], amma hakan ba a hannuna yake ba. Yana hannunsu. Ba wai ina tambaya ba ne a cika mini wasu sharuda masu girman gaske," a cewar Salah a hirarsa da GQ.

Salah, wanda ya taimaka wa Liverpool ta yi nasara a Gasar Zakarun Turai da kuma ta Firimiyar Ingila tun da ta saye shi a 2017, ya kara da cewa: "Batun shi ne, idan ka bukaci a ba ka wani abu kuma suka nuna maka cewa za su iya ba ka wani abin, [ya kamata su yi hakan] saboda su nuna cewa sun yaba da abubuwan da ka yi wa kungiyar.

"Na kasane a wannan kungiyar tsawon shekaru biyar kenan. Na san wannan kungiyar sosai. Ina kaunar magya bayanta. Su ma suna kaunata.

"Amma an gaya wa masu gudanar da harkokin kungiyar halin da ake ciki. Yanzu komai a hannunsu yake."

Da aka tambaye shi ko burinsa ne ya zama gwarzon dan kwallon duniya, Salah, wanda ya ci wa Liverpool kwallo 148, ya ce: "Idan ka tambaye ni ko hakan ne ya sa na zo nan, zan ce eh, tabbas.

"Gaskiya ba zan yi karya ba kuma a hakikanin gaskiya ban yi tunani a game da haka ba. Ina son zama gwarzon dan kwallon duniya. Amma zan yi rayuwa mai kyau ko da ban lashe kyautar Ballon d'Or ba. Rayuwa na tafiya daidai, komai yana tafiya yadda ya kamata."

A halin yanzu Salah yana Afirka inda yake fafatawa a gasar cin kofin nahiyar.

Liverpool banner footer

Asalin hoton, BBC Sport