Afcon 2022: Karawa tsakanin Habasha da Cape Verde a rukuinin farko

Asalin hoton, AFP
Za a buga wasa na biyu tsakanin Habasha da Cape Verde a Olembe da ke Yaounde da zarar an tashi wasan Kamaru da Burkina Faso ranar Lahadi.
Wasannin rukunin farko
Lahadi 9 ga watan Janairu: Kamaru da Burkina Faso, Habasha da Cape Verde
Alhamis 13 ga watan Janairu: Kamaru da Habasha, Cape Verde da Burkina Faso
Litinin 17 ga watan Janairu: Burkina Faso da Habasha, Cape Verde da Kamaru
Wadan nan kasashen biyu za su fuskanci kalubale a wajen Kamaru mai masaukin baki da ke fatan lashe kofi na shida jumulla, kuma a karon farko a gida, bayan da shekara 50 da ta karbi bakuncin wasannin gasar, amma bata dauki kofin ba.
Wasa na biyu a cikin rukuni
Rana: 9 ga watan Janairun 2022
Lokaci: 20:00 agogon Kamaru (19:00 GMT)
Wuri: Olembe Stadium, Yaounde

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar kwallon kafa ta Habasha
Habasha za ta buga Afcon a bana, wadda rabon da ta je gasar tun 2013.
Sau nawa ta je gasar: Karo na 11Kwazon da ta yi: Ta lashe kofin a 1962
Koci: Wubetu Abate Kyaftin: Getaneh Kebede
Matakinta a Fifa: 137Sunan da ake kiranta: Walia Ibex
Habasha na fatan dawo da karsashinta a gasar kwallon Afirka mai kofi daya, wadda tana daga cikin wadanda suka kafa wasannin da yi masa fasali.

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar kwallon kafa ta Cape Verde
Sau nawa ta jee gasar:3Kwazon da ta yi: Quarter-finals a 2013
Koci: Bubista Kyaftin: Ryan Mendes
Matsayi a Fifa: 73 Sunan da ake kiranta: Blue Sharks
Cape Verde za ta buga Afcon karo na uku, wadda ta fara zuwa gasar daga 2013, kuma tana fatan taka rawar ganii kafin ta fuskanci Kamaru mai masaukin baki da kuma Burkina Faso.
'YAN WASAN TAWAGAR HABASHA
Masu tsaron raga: Teklemariam Shanko (Sidama Coffee, Ethiopia), Fasil Gebremichael (Bahir Dar Ketema, Ethiopia), Jemal Tassew (Adama Ketema, Ethiopia).
Masu tsaron baya: Asrat Tunjo (Ethiopian Coffee, Ethiopia), Suleiman Hamid (St George, Ethiopia), Remedan Yesouf (Wolkite K, Ethiopia), Desta Yohannes (Adama K, Ethiopia), Aschalew Tamene (Fasil K, Ethiopia), Yared Bayeh (Fasil K, Ethiopia), Mignot Debebe (St George, Ethiopia), Menaf Awol (Bahir Dar K, Ethiopia).
Masu buga tsakiya: Amanuel Yohannes (Ethiopian Coffee, Ethiopia), Gatuoch Panom (St George, Ethiopia), Shemeles Bekele (El Gouna, Egypt), Mesoud Mohammed (Jimma AJ, Ethiopia), Fitsum Alemu (Bahir Dar K, Ethiopia), Firew Solomon (Sidama Coffee, Ethiopia), Bezabeh Meleyou (Fasil K, Ethiopia).
Masu cin kwallaye: Abubeker Nassir (Ethiopian Coffee, Ethiopia), Getaneh Kebede (Wolkite K, Ethiopia), Amanuel Gebremichael (St George, Ethiopia), Shemeket Gugsa (Fasil K, Ethiopia), Mujib Kassim (JS Kabylie, Algeria), Mesfin Taffese (Hawassa K, Ethiopia), Dawa Hotessa (Adama K, Ethiopia).
'YAN WASAN TAWAGAR CAPE VERDE
Masu tsare raga: Vozinha (AEL Limassol, Cyprus), Marcio da Rosa (Montalegre, Portugal), Keven Ramos (Mindelese, Cape Verde), Elber Evora (AEL Limassol, Cyprus).
Masu tsare baya: Stopira (Fehervar, Hungary), Steven Fortes (Oostende, Belgium), Jeffry Fortes (De Graafschap, Netherlands), Steve Furtado (Beroe, Bulgaria), Roberto Lopes (Shamrock Rovers, Republic of Ireland), Joao Paulo Fernandes (Feirense, Portugal), Diney Borges (AS Far, Morocco), Ponck (Istanbul Basaksehir, Turkey), Dylan Tavares (Neuchatel Xamax, Switzerland), Delmiro Nascimento (Aris Limassol, Cyprus).
Masu buga tsakiya: Kenny Rocha (Oostende, Belgium), Nuno Borges (Casa Pia, Portugal), Patrick Andrade (Qarabag, Azerbaijan), Jamiro Monteior (Philadelphia Union, USA), Nenass (Aalesund, Norway), Marco Soares (Arouca, Portugal).
Masu cin kwallaye: Ryan Mendes (Al Nasr, UAE), Willy Semedo (Pafos, Cyprus), Gilson Tavares (Estoril-Praia, Portugal), Willis Furtado (FK Jerv, Norway), Julio Tavares (Al Faisaly, Saudi Arabia), Garry Rodrigues (Olympiakos, Greece), Lisandro Semedo (Fortuna Sittard, Netherlands), Vagner (Sion, Switzerland).












