Messi ya cika shekara 39: Ta yaya shi da Ronaldo ke ci gaba da kafa tarihi?

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lionel Messi, mai shekara 39 da Cristiano Ronaldo mai shekara 41, sun kaffa sabbin tarihi a gasar cin kofin duniya a 2026
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Tabbas wannan ce gasar cin kofin duniya ta karshe da suke bugawa a tsakaninsu, kuma karo na shida da kowanne ke halarta

Duk da haka Lionel Messi - wanda ke murnar cika shekara 39 a ranar Laraba - da Cristiano Ronaldo - mai shekara 41 - ba su nuna wata alamar gajiyawa ba a babban matakin taka leda a duniya.

Ƙwallaye biyu da Messi ya ci Austria ranar Litinin a wasa na biyu a cikin rukuni, sun sa ya ci 18 jimilla, hakan ya zama shi ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a raga a tarihin babbar gasar tamaula ta duniya.

A lokaci guda kuwa, Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko da ya zura ƙwallo a gasar kofin Duniya guda shida daban-daban, sakamakon biyun da ya zura a ragar Uzbekistan ranar Talata da suka yi nasara 5-0 a wasa na bibiyu a cikin rukuni.

Lokacin da Messi ya ci wa Argentina ƙwallo uku rigis a wasan farko da Aljeria, sannan ya kara biyu a ragar Austria a daren Litinin, sai Ronaldo ya fuskanci matsin lamba, saboda bai ci ƙwallo ba a wasan farko a cikin rukuni da suka buga da Congo DR, inda suka tashi 1-1.

Tsohon ɗan wasan Real Madrid, ya fuskanci matsin lamba da kuma yaɗa jita-jita da cewar ya samun matsala a dangantaka da wasu daga cikin abokan wasansa na Portugal. Amma sai ya mayar da martani da cin ƙwallo biyu a karawar da ta sa ya kara shiga kundin tarihi.

Mintuna shida da fara wasa tsakanin Portugal da Uzbekistan, Ronaldo ya fara zura ƙwallo a raga, hakan ya sa ya kafa tarihin cin ƙwallo a gasar Kofin Duniya karo na shida tun daga gasar 2006 da 2010 da 2014 da 2018 da 2022 da kuma 2026, babu wanda ya ya yi wannan bajintar.

Ɗan wasan da ya halarci gasar kofin duniya karo na shida a bana har da Messi, amma bai ci ƙwallo ba a gasar 2010 da aka gudanar a Afirka ta Kudu, wadda Sifaniya ta lashe.

Kwallayen da Ronaldo ya ci Uzbekistan sun kawo ƙarshen jerin wasa 11 a Kofin Duniya ba tare da ya zura ƙwallo ba a raga, tun daga wasan buɗe Kofin Duniya a 2022 a karawa da Ghana.

Shin ko Ronaldo yana damuwa kan kokarinsa a tamaula? Abin da ya faɗa bayan an tashi wasan - yana mai cewa "Na dawo" kai tsaye ya fuskanci ƙyamara ya faɗi kalaman - ya nuna irin fama da ɗan wasan ya fuskanta, wanda ke fatan sake yin irin gagarumin tasirin da ya taba yi a baya.

"Shi ma mutum ne," in ji kocinsa, Roberto Martinez bayan da aka kammala karawar. "Yana da 'yancin jin raɗaɗi da damuwa a tare da shi."

"Wannan shi ne abin da yake yi," in ji tsohon takwaransa wanda suka taka leda tare a Manchester United, Wayne Rooney kamar yadda ya sanar da BBC Sport. "Yakan sha suka, kuma da haka yake sawa ya mayar da hankali kan fuskantar kalubale da mayar da martani."

A cikin shekara ashirin da suka gabata, ba a sami lokutan da Ronaldo ya "sake" hawa kololuwar ganiyarsa ba.

Yanzu shi ne ɗan wasa na biyu mafi tsufa da ya zura kwallo a tarihin Kofin Duniya yana da shekara 41 da kwana 138, mai rike da ƙwazon shi ne ɗan kasar Kamaru, Roger Milla mai shekara 42 da kwana 39.

Ƙwallaye biyun da Ronaldo ya zura a raga ranar Litinin, ya kuma zama ɗan wasa na uku da yake da tarihin cin ƙwallo a matakin matashi da kuma wanda ya fi tsufa a tawagar kasa a gasar cin kofin duniya.

Masu rike da wannan tarihin sun haɗa da ɗan kasar Denmark, Denmark Michael Laudrup da kuma Messi.

Ronaldo da Messi sun ci wa kasashensu ƙwallo a wasansu na farko da na karshe a gasar kofin duniya shekara 20 da kwana 11 tsakani daga lokacin da aka haɗa wannan rahoton.

"Ban damu da abin da wasu ke yi ba ko kaɗan" - Ronaldo

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Messi ya ci ƙwallo 12 a gasar kofin duniya tun daga lokacin da ya cika shekara 35
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Ba na damuwa da abin da wasu ke yi," in ji Ronaldo a lokacin da yake tattaunawa da ƴan jarida ranar Talata, bayan da aka tambaye shi game da ƙwallaye biyar da Messi ya ci a wasa biyu da fara gasar cin kofin duniya … "Mbappe ma ya zura ƙwallaye."

Ɗan wasan Portugal ya ce ganin manyan taurarin ƙwallon ƙafa na duniya suna haskakawa a wannan gasar cin kofin duniya ya hakan wata hanya ce da ta ƙarfafa masa gwiwa. Musamman Messi.

"Na yi imani duka ƴan wasan biyu sun inganta ƙwallon ƙafa a tsawon shekaru, kuma hamayya da take tsakaninsu ta yi mahimmanci wajen haɓaka wasanninsu," in ji Martinez.

Ronaldo da Messi sun ci gaba da ƙalubalantar juna, hakan ne ya sa a koda yaushe ake ta muhawarar wanene kan gaba a tsakaninsu a fagen taka leda a duniya.

Tun bayan da ya kai shekara 35, Messi ya samu sabon matsayi a fagen ƙwallon ƙafa, wanda ya zura kwallaye 12 a wasa tara a gasar Kofin Duniya.

Wannan ya sa ya zarce ƙwallo 10 da Ronaldo ya ci ya bashi tazarar biyu tsakani, hakan ya sa ya yi kan-kan-kan da Pele mai 12 a raga mai shekara 35.

Messi ya zura kwallaye shida ne a raga a wasa 19 a gasar, tsakanin shekara 18 zuwa 34.

Sauyin wannan yanayi ya faru ne tun bayan da ya bar Barcelona. Ana iya cewa watakila ya fi mayar da hankali wajen taka leda ga Argentina, bayan barin Barcelona, wanda a baya ake sukarsa da cewa ya fi damuwa da ci gaban Barcelona maimakon kasarsa.

Mutane da dama sun yi iƙirarin cewa bai yi hakan ba lokacin da yake taka leda a manyan gasar Turai a mafi kyawun shekarunsa.

Tun bayan da ya kai shekara 35, Ronaldo ya zura kwallo takwas a wasa16 a gasar Kofin Duniya da ta Kofin Nahiyar Turai.

Har yanzu Ronaldo yana fatan cin ƙwallo 1,000a ƙungiya da tawaga, kafin ya yi ritaya, idan ka haɗa lissafi da biyun da ya ci Uzbekistan yana da 975 jimilla, kenan yana bukatar 25 nan gaba.

Idan ka auna hamayya tsakanin Ronaldo da Messi, an daina maganar lashe Ballon d'Or, ko fuskantar kalubalen manyan ƙungiyoyin Turai, domin dukkansu ba sa taka leda a Turai, Ronaldo yana Saudiyya da taka leda, Messi yana Amurka a gasar MLS, Amma har yanzu ƙoƙarinsu na yin takara da juna mataki-mataki har yanzu yana ɗaukar hankali.

Watakila ƴan wasan biyu su fuskanci juna a gasar kofin duniya a bana, hakn zai faru ne idan Portugal da Argentina kowacce ta lashe wasanta na rukuni da yin nasara a zagayen ƴan 32 da kuma na ƴan 16 daga nan za su kara a zagayen kwata fainal ranar 11 ga watan Yuni a birnin Kansas, kuma ƴan kallo za si fatan hakan.

Haka kuma watakila mu gansu a gasar 2030 suna ta hamayya da kokarin ci gaba da kafa sabbin tarihi a fannin taka leda a duniya.