Jurgen Klopp bai ji dadin sauya lokacin Afcon ba

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Salah, Keita da Mane
An wallafa

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce matsar da gasar cin kofin nahiyar Afirka ta Afcon zuwa watan Janairu zai yi wa kungiyar tasa 'illa'.

An dai sauya lokacin gasar da za a yi a 2021 ne daga lokacin bazara zuwa na hunturu saboda yanayi 'maras dadi' da Kamaru mai masaukin baki za ta fuskanta a lokacin.

Hakan yasa kungiyar ta Liverpool za ta yi rashin 'yan wasanta na Afirka har na tsawon wata guda a dai-dai lokacin da ake tsaka da taka wasannin Premier Ingila na kaka mai zuwa.

'Yan wasan dai su ne Sadio Mane na Senegal da Mohamed Salah na Misra da Naby Keita na Guinea.

Jurgen Klopp ya ce "Idan har akwai bukatar kawo wani dan wasa ya cike gurbinsu, to ba karamin dan wasa za mu kawo ba.

Saboda rashin 'yan wasan na tsawon makonni hudu, dole ne kulob ya damu."

Gasar ta Afcon da aka yi a Misra a 2019 ce ta farko da aka yi a lokacin bazara sabanin yadda ake yin ta a baya a watannin Janairu da Fabrairu.

Shawarar da aka yanke a 2017 ta sauya lokacin wasannin na Afcon zuwa watan Yuni ta samu karbuwa musamman a tsakanin kungiyoyin wasan kasashen Turai.