Gwamnatin Oyo ta saka dokar hana fita a ƙananan hukumomi 10

Asalin hoton, Seyi Makinde/X
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da sanya dokar hana fita na sa'o'i 16 a wasu ƙananan hukumomi 10 kan matsalar tsaro a jihar.
Sanarwar da sakataren gwamnatin Jihar, Farfesa Musibau Babatunde ya fitar ta ce dokar za ta fara aiki daga yau, ranar Laraba, 24 ga watan Yuni, 2026, kuma za ta kasance tsakanin karfe 4 na yamma zuwa karfe 8 na safe na tsawon sa’o’i 16 a matakin farko.
Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Oriire da Orelope da Irepo da Saki West da Saki East da Atisbo da Itesiwaju da Iseyin da Olorunsogo da kuma Atiba, musamman waɗanda ke kusa da gandun dajin Old Oyo National Park.
Wannan mataki ya biyo bayan zanga-zangar da ta ɓarke a jihar sakamakon sace yara da malamai a yankin Oriire a watan Mayu, inda masu zanga-zangar suka buƙaci gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa domin ceto waɗanda aka sace tare da kawo karshen matsalar tsaro a faɗin kasar.
















