Afcon 2021: Hakim Ziyech ba zai buga gasar kofin Afirka ba

Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon Chelsea, Hakim Ziyech baya cikin 'yan tawagar kwallon kafar Morocco da za su buga mata gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi daga watan Janairu.
Mai shekara 28, bai buga dukkan wasa shida da Morocco ta kara a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya ba a bana, wanda rabon da ya yi wa Atlas Lions tamaula tun wasan sada zumunta da Burkina Faso cikin watan Yuli.
Cikin 'yan wasan Premier League da ke tawagar Morocco har da Romain Saiss na Wolverhampton da biyu daga Watford, Adam Masina da Imran Louza da kuma mai taka leda a QPR, Ilias Chair.
Haka kuma tawagar ta gayyaci dan wasan Paris St-Germain, mai tsaron baya, Achraf Hakimi.
Morocco tana rukuni na uku da ya hada da Ghana da Comoros da kuma Gabon a gasar da Kamaru za ta karbi bakuncin wasannin da za a fara daga 9 ga watan Janairun zuwa 6 ga watan Fabrairu.
'Yan wasan Morocco da za su buga mata kofin duniya:
Masu tsaron raga: Yassine Bounou (Sevilla, Spain), Monir El Kajoui, (Hatayspor, Turkey), Anas Zniti (Raja Casablanca, Morocco).
Masu tsaron baya: Achraf Hakimi (Paris Saint-Germain, France), Sofiane Alakouch (Metz, France), Souffian El Karouani (NEC Nijmegen, Netherlands), Adam Masina (Watford, England), Sofian Chakla (OH Leuven, Belgium), Samy Mmaee (Ferencvaros, Hungary), Romain Saiss (Wolves, England), Nayef Aguerd (Rennes, France).
Masu buga tsakiya: Aymen Barkok (Eintracht Frankfurt, Germany), Sofyan Amrabat (Fiorentina, Italy), Faycal Fajr (Sivaspor, Turkey), Azzedine Ounahi (Angers, France), Ilias Chair (QPR, England), Imran Louza (Watford, England), Selim Amallah (Standard Liege, Belgium).
Masu cin kwallaye: Munir El Haddadi (Sevilla, Spain), Zakaria Aboukhlal (AZ Alkmaar, Netherlands), Abdessamad Ezzalzouli (Barcelona, Spain), Sofiane Boufal (Angers, France), Ryan Mmaee (Ferencvaros, Hungary), Youssef En-Nesyri (Sevilla, Spain), Ayoub El Kaabi (Hatayspor, Turkey).











