Yadda Fulani ke fargaba a kudancin Najeriya bayan satar daliban Oyo

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyoyin Fulani a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya sun yi gargadin cewa zargin kabilar Fulani da hannu a ayyukan garkuwa da mutane ba tare da hujja ba na iya haifar da rikicin kabilanci da kuma dagula zaman lafiya a yankin.
Kungiyoyin sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Oyo da su gargadi mai fafutukar kare hakkin Yarabawa, Sunday Igboho, kan kalaman da suka ce na iya haddasa rashin jituwar kabilanci.
Wannan na zuwa ne bayan da Sunday Igboho ya bai wa masu garkuwa da mutane wa'adin sa'o'i biyu su sako wasu daliban da aka sace a Jihar Oyo, tare da yin barazanar daukar mataki idan ba a sake su ba.
A wata sanarwa da kungiyar Fulani ta fitar, ta ce abin damuwa ne yadda ake alakanta duk wani laifin garkuwa da mutane da Fulani, lamarin da ta ce na iya jefa rayukan Fulani mazauna yankin cikin hadari.
Kungiyar ta ce mafi yawan Fulani a yankin makiyaya ne da ke gudanar da harkokinsu cikin lumana, don haka bai dace a dora laifin wasu tsiraru kan daukacin al'umma ba.
Sai dai Sunday Igboho ya musanta zargin cewa yana nuna wariya ko kuma kokarin tunzura rikicin kabilanci.
A cewarsa, fafutukarsa ba ta da alaka da kabila ko addini, illa neman a magance matsalar tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin al'ummar yankin.
"Ba Fulani nake fada da su ba, masu aikata laifi ne nake magana a kansu. Duk wanda ya shiga harkar garkuwa da mutane ko ta'addanci dole a dauki mataki a kansa," in ji shi.
Masu sharhi kan harkokin tsaro sun yi gargadin cewa kalamai masu nasaba da kabila na iya kara tsananta rashin amincewa tsakanin al'ummomi, tare da jaddada muhimmancin hukumomi su gudanar da bincike tare da hukunta masu laifi ba tare da la'akari da asalinsu ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sabuwar takaddamar ta samo asali ne bayan garkuwa da wasu dalibai da malamansu a wasu makarantu da ke Jihar Oyo, lamarin da ya haddasa fargaba da tashin hankali a tsakanin iyaye da mazauna yankin.
Batun ya kara daukar hankali ne bayan Sunday Igboho ya shiga cikin lamarin, inda ya zargi wasu da hannu a satar tare da yin kira ga hukumomi da su dauki matakin gaggawa domin kubutar da wadanda aka sace.
A cikin wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta, an ga Sunday Igboho yana ganawa da wasu shugabannin al'umma da kuma Fulani a yankin, inda ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke kara kamari.
Sai dai kalaman nasa sun jawo martani daga wasu kungiyoyin Fulani da ke ganin cewa ana kokarin alakanta kabilar Fulani da laifukan da wasu tsirarun mutane ke aikatawa.
Masu lura da al'amuran yau da kullum sun ce damuwar da kungiyoyin Fulani ke nunawa ba sabon abu ba ne, duba da yadda a baya aka samu tashin hankali tsakanin wasu al'ummomi da makiyaya a sassa daban-daban na kasar.
A shekarun baya, rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a jihohin Benue, Plateau, Kaduna da wasu sassan Kudu maso Yammacin Najeriya sun yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.
Wannan ne ya sa wasu ke fargabar cewa duk wani yunkuri na alakanta matsalar tsaro da wata kabila ka iya kara ruruta wutar rashin amincewa tsakanin al'ummomin da suka dade suna rayuwa tare.

Asalin hoton, Getty Images
A cikin 'yan shekarun nan, garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ta zama daya daga cikin manyan kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta.
Daga Arewa maso Yamma zuwa Arewa ta Tsakiya, har zuwa wasu sassan Kudu maso Yamma, masu garkuwa da mutane na ci gaba da kai hare-hare kan makarantu.
Lamarin ya raba kan jama'a, inda wasu ke goyon bayan matakan da Sunday Igboho ke dauka saboda suna ganin hukumomi ba sa yin abin da ya kamata wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Sai dai wasu kuma na ganin cewa ko da yake matsalar tsaro na bukatar daukar mataki cikin gaggawa, ya kamata a guji kalaman da za su iya haddasa rashin jituwa tsakanin kabilu.
Ya zuwa yanzu hukumomin Jihar Oyo ba su ce komai ba kan bukatar da kungiyoyin Fulani suka yi na a gargadi Sunday Igboho ba.
Sai dai gwamnatin jihar ta sha nanata kudirinta na yin aiki tare da hukumomin tsaro domin dakile ayyukan masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka.
Haka kuma jami'an tsaro sun yi kira ga jama'a da su ci gaba da bayar da bayanan sirri da za su taimaka wajen gano masu hannu a satar mutane da sauran laifuffuka.
A halin yanzu dai hankulan mutane na kan kokarin kubutar da wadanda aka sace da kuma matakan da gwamnati da jami'an tsaro za su dauka domin hana sake aukuwar irin wadannan hare-hare a nan gaba.










