An tsayar da ranar wasan Real Madrid da Atletico Madrid

Real Madrid

Asalin hoton, Real Madrid FC

An wallafa

Hukumar da ke kula da gasar La Liga ta tsayar da ranar buga wasan hamayya tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid a Santiago Bernabeu.

An tsayar da ranar 12 ga watan Disamba, domin fafatawa a wasan mako na 17 a babbar gasar ta Sifaniya.

Kungiyoyin biyu sun kara a bara, inda Real Madrid ta doke Atletico da ci 2-0 ranar 12 ga watan Disambar 2020.

A wasa na biyu kusa suka tashi 1-1 ranar 7 ga watan Maris din 2021 a gidan Atletico Madrid.

Real Madrid mai kwantan wasa tana mataki na biyu da maki 27 da tazarar maki daya tsakaninta da Real Sociedad wadda ke jan ragama.

Ita kuwa Atletico Madrid mai itama kwantan wasa mai rike da kofi tana ta hudu da maki 23 a teburin La Liga na bana.

Ranar Asabar Barcelona za ta karbi bakuncin Espanyol, wasan farko da sabon koci Xavi Hernandez zai ja ragamar kungiyar, wadda take ta tara da kwantan wasa.

Ranar Laraba Barcelona ta gabatar da Dani Alves a matakin dan wasan da zai taka mata tamaula a karo na biyu.

Sai dai kuma dan kwallon tawagar Brazil ba zai buga wa Barcelona gasa ba har sai cikin watan Janairun 2022.

Wasannin mako na 13 da za a fatata tun daga ranar Juma'a

Ranar Juma'a 19 ga watan Nuwamba

Levante da Athletic Bilbao

Ranar Asabar 20 ga watan Nuwamba

  • Celta de Vigo da Villarreal C
  • Sevilla da Deportivo Alaves
  • Atletico Madrid da Osasuna
  • FC Barcelona da Espanyol

Ranar Lahadi 21 ga watan Nuwamba

  • Getafe da Cadiz
  • Granada da Real Madrid
  • Elche da Real Betis
  • Real Sociedad da Valencia

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a gasar La Liga:

  • Karim Benzema Real Madrid 10
  • Luis Suarez Atletico Madrid 7
  • Vinicius Junior Real Madrid 7
  • Raul De Tomas Espanyol 7
  • Memphis Depay Barcelona 6
  • Mikel Oyarzabal Real Sociedad 6
  • Jose Luis Sanmartin Mato Deportivo Alaves 5
  • Iago Aspas Celta de Vigo 5
  • Arnaut Danjuma Groeneveld Villarreal 5
  • Willian Jose Real Betis 5
  • Juan Miguel Jimenez Lopez Real Betis 5
  • Radamel Falcao Rayo Vallecano 5