Manchester United 1-1 Everton: Andros Townsend ne ya farke kwallon a Old Trafford

An wallafa

Andros Townsend ne ya farke kwallon da ya bai wa Eveton maki a karawar Premier League wasan mako na bakwai da Manchester United a Old Trafford da suka tashi 1-1.

Anthony Martial ne ya fara ci wa United kwallo tun kan hutu, kuma na farko da ya zura a raga tun cikin watan Fabrairu.

Everton ta farke ne bayan da Demarai Gray ya hada jiki da Fred da kuma Wan-Bissaka, sannan ya ja kwallo ya bai wa Abdoulaye Doucoure, shi kuma ya buga waTownsend, wanda ya zura a ragar United.

Townsend ya ci kwallo biyar kenan a wasa tara da ya buga wa Everton a dukkan fafatawa.

Da wannan sakamakon an zura kwallo a kalla daya a wasa tara a Old Trafford kenan a karon farko tun bayan 10 da ta yi wannan rashin kokarin a Fabrairun 1971.

Sakamakon nan zai kara jefa Ole Gunnar cikin matsi, wanda ya yi rashin nasara a hannun Aston Villa makon da ya wuce da kuma fitar da United daga League Cup da West Ham United ta yi.

Manchester United za ta buga wasan gaba a Premier League da Leicester ranar Asabar 16 ga watan Oktoba, ita kuwa Everton za ta kece raini da West Ham ranar Lahadi 17 ga watan Oktoba.